Daga Ibrahim Muhammad, Kano A yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar Ilim, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an ...
A yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar Ilim, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an fitar da Naira Biliyan Uku don gina sabbin ajujuwa a makarantu a dukkan Ƙananan HukumomiN na jihar.
A taron da aka gudanar ranar Tallata, Gwamnan ya ce aikin za a yi ne domin kyautata yanayi mai kyau na koyo da koyarwa ga ɗaliban jihar.
Sannan kuma ya ce, za a ɗauki ma’aikata dubu 17 da za su riƙa gadin makarantun Firamare a kowace Ƙaramar Hukuma.
Ya ce, matakin tsarin ɗaukar masu gadin za a yi ne daga unguwannin da makarantun suke don a tabbatar da suna aikinsu yadda ya kamata.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kowacce Ƙaramar Hukuma za ta karɓi Naira Miliyan 25 na gyaran makarantu, inda hukumar kula da ilimin bai-ɗaya ce za ta sanya idanu kan yadda ake gudanar da ayyukan domin tabbatar da an yi mai nagarta.
No comments