Daga Ibrahim Muhammad, Kano A halin da ake ciki dai dambarwar masarautar Kano ta sake ɗaukar wani sabon salo, inda a jiya Lahadi, jami'a...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
A halin da ake ciki dai dambarwar masarautar Kano ta sake ɗaukar wani sabon salo, inda a jiya Lahadi, jami'an 'yan sanda suka fatattaki duk wani ɗan Tauri da ke fadar Sarkin Kano, inda yanzu jami'an ne ke sintiri a harabar Fadar.
Su dai waɗannan nan 'yan Tauri da yanzu kowa ya kama gaban sa, su ne suke gadin Sarki Muhammadu Sanusi II tun bayan da gwamnatin jihar ta dawo da shi bisa karagar mulki.
Tun a watan da ya gabata ne aka ƙaro yawan 'yan Taurin don tsare Fadar ta Muhammadu Sanusi, lokacin da aka yaɗa jita-jitar cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin dawo da Aminu Ado Bayero cikin Fadar ko da ƙarfin tsiya.
Duk da wannan hali da ake ciki, shi kuma Sarki Alhaji Aminu Ado Bayeri yana can Fadar sa ta Nasarawa, inda jami'an tsaro ne ke gadin sa, duk da kuwa umurnin da gwamnatin jihar ta ba shi na ya fice daga gidan.
Tuni dai Sarakunan biyu, kowa ke gudanar da harkokin sa a maysayin Sarkin Kano.
No comments