Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Raba Buhunan Taki 59,205 Ga Manoma, Ya Ce Noma Shi Ne Jigon Tattalin Arzikin Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake jaddada cewa noma ya kasance jigon tattalin arzikin jihar. A ranar Laraba ne gwamnan ya ƙaddamar ...


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake jaddada cewa noma ya kasance jigon tattalin arzikin jihar.

A ranar Laraba ne gwamnan ya ƙaddamar da rabon kayayyakin noma na shekarar 2025 na damina tare da ƙaddamar da sabon gidan Fadama, wanda aka gudanar a Ma’aikatar Noma da ke Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce an ƙaddamar da motocin taki guda 98 don raba wa manoma domin noman damina.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470.

A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara.

Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne.

“Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da fifiko a matsayinmu na al’umma, sama da kashi 85 na al’ummarmu sun dogara ne kan noma don rayuwa. Haƙƙin ne a kan mu, kuma haƙiƙa ya zama wajibi mu ba su goyon baya da ƙarfafa su.

“Wannan gwamnatin tana kallon noma a matsayin dabarar samar da abinci, samar da ayyukan yi, rage fatara, da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya, shi ya sa muke aiwatar da shirin kawo sauyi a fannin noma, wanda ya dace da buƙatun al’ummominmu da kuma yin daidai da manufar ci gaba mai ɗorewa ta 2, wanda ke neman kawo ƙarshen yunwa, inganta abinci mai gina jiki, da bunƙasa noma mai ɗorewa.

"Duk da ƙalubalen sauyin yanayi da kuma ƙarshen lokacin damina na 2025, mun ci gaba da mai da hankali sosai, gwamnatinmu tana tallafa wa manoma da kayan aikin da ake buƙata don bunƙasa noma da samun kuɗin shiga, muna saka hannun jari a fannin samar da iri, takin zamani, fasaha, da jarin bil'adama don samun tasiri na dogon lokaci.

“Manufarmu ta haɗa da ƙarfafa mata, matasa, da kuma ɗaiɗaikun mutane masu buƙatu na musamman a matsayin wakilai na kawo sauyi, ba wai mahalarta kaɗai ba. Mun bullo da ingantaccen tsarin rabo cikin gaskiya don tabbatar da cewa tallafin ya isa ga manoman da suka dace a daidai lokacin da ya dace.

"Mun gane cewa manoma na fuskantar matsaloli kamar rashin damar samun kayan aiki, kuɗaɗe, rashin tabbas na kasuwa, asarar bayan girbi, da kuma tasirin sauyin yanayi. Amma muna tunkarar waɗannan batutuwa.

“Ta hanyar shiga tsakani, muna gina tsarin da zai taimaka wa manomanmu daga shuka har zuwa bayan girbi. Muna haɓaka noma da injinan zamani.

“Bari na dan ɗauki lokaci in yi magana kai tsaye ga waɗanda suka ci gajiyar shirin na bana. Waɗannan kayayyakin ba na sayarwa be ne. Ba kayayyakin da za a yi ciniki da su ba ne domin a samu ci gaba cikin gaggawa. Kayan aiki ne na samar da ci gaba, zuba jari a nan gaba da kuma makomar Zamfara. Ku yi amfani da su cikin hikima, ku yi amfani da su cikin gaskiya, ku bar su su zama ginshiƙi na ƙaruwar girbi da inganta rayuwa.

“Baƙi masu girma, ’yan uwa maza da mata, yanzu ya zama abin alfaharina na ƙaddamar da shirin Rarraba Kayayyakin Aikin Noma na 2025 a hukumance, wanda zai amfani ƙananan manoma 59,205 a faɗin jihar mu.”
 

No comments