Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Malam Abdulaziz Abdulaziz: Gudumawa Sa A Matsayin Hadimi Na Musamman Ga Shugaban Ƙasa Tinubu

 Daga Bashir Abdullahi El-Bash -Ya Shiga Ya Fita Ya Samar Wa Ɗumbin Matasa Ayyukan Yi Da Damammaki Cikin Gwamnati. -Ya Riƙe Wa Shugaban Ƙasa...


 Daga Bashir Abdullahi El-Bash


-Ya Shiga Ya Fita Ya Samar Wa Ɗumbin Matasa Ayyukan Yi Da Damammaki Cikin Gwamnati.

-Ya Riƙe Wa Shugaban Ƙasa Masoya Ya Ƙarfafa Musu Gwiwar Ci Gaba Da Kasancewa A Bayan Tafiyarsa

-Ya Riƙe Wa Shugaban Ƙasa Maƙiya Ya Hana Su Suka Da Yaƙarsa.

A yau, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin sadarwa, Mallam Abdulaziz Abdulaziz ya cika shekaru biyu daidai a kan wannan muƙami da shugaban ƙasa ya ba shi.

Da ji ko da gani, za mu fahimci cewa ba shakka kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin waɗannan shekaru biyu da ya shafe a kan wannan matsayi.

Domin kuwa yayi amfani da damarsa wajen samowa ɗumbin matasa ayyukan yi da sauran damammaki na romon dimokaraɗiyya.

Ayyukan alkhairinsa ba ga iya masoya shugaban ƙasa Tinubu kaɗai suka tsaya ba, kowa da kowa yake amfanawa. Wannan tasa hakan ya taimaka wajen riƙewa shugaban ƙasa Tinubu masoya waɗanda har yanzu suke tsaye a bayansa. Sannan kuma ya riƙe masa ƴan adawa waɗanda saboda shi suke kasa motsa adawarsu ko yaƙarsa. Irin namijin ƙoƙarin da ba kowane mai riƙe da muƙamin siyasa ne ya yi shugaban ƙasa shi ba a duk Arewa.

A matsayin Mallam Abdulaziz Abdulaziz na jajirtaccen ma’aikaci mai kula da harkokin sadarwa da ke yi wa shugaban ƙasa aiki, ya samar da kykkyawar alaƙa da fahimta mai kyau tsakaninsa da ƴan Jaridu da sauran mutanen da ke ayyukan yaɗa labarai. Wannan alama ce da ke nuni da yadda yake girmama ƴan jaridu da mutunta su gami da ba su kulawa ta musamman a matsayinsa na wanda ya fito daga cikinsu, hakan ya nuna cewa shi ɗin ɗan halak ne wanda ba ya manta mafari.

Duk da cewa Mallam Abdulaziz Abdulaziz ya yi ayyuka da dama na taimakon al’umma da gina rayuwar mutane, wasu abubuwan ma in yayi ba ya son a sani ko a ce shi ya yi. Wannan ke nuna yadda ya kasance mutum mai tsarkin Zuciya da kuma yin alheri ba dan a saka masa ba, sai don kishin ƙasa da son gina mutane.

Amma dai duk da haka, komai jimawa muna da kykkyawan fatan sai ya girbi abin da ya shuka na alheri, domin alheri ba ya faɗuwa ƙasa banza.

Mallam Abdulaziz Abdulaziz ya tona asirin mutane da dama da suka samu irin wannan damammaki a baya ba su taimaki al’umma ba.

A cikin waɗannan shekaru biyu, ya yi abubuwan da wasu ba su yi ba a shekaru 4-8 a gwamnatocin baya. Shi ne mutum na farko da ya fara nunawa al’umma muhimmancin dama da yadda ake amfani da ita. Ya share hawayen dubban matasa sun tsaya da ƙafafunsu, ya kuma zame Garkuwa ga shugaban ƙasa Tinubu da gwamnatinsa wanda hatta ƴan adawa suke shakkar yin adawa saboda shi.

A madadin ni kaina, Bashir Abdullahi El-Bash, ina taya shi murnar cika wannan shekaru biyu a kan wannan muƙamin, yadda ya fara da Bismillah Allah Ya sa ya kammala da Hamdala. Allah Ya nunka masa dama sama da wannan a rayuwa ta gaba.

No comments