Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tallafa Wa Mata : PAN Takarrama Matar Gwamnan Zamfara

Daga Hussaini Yero, Funtua Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karɓi lambar yabo a karo na biyu daga ƙungiyar ...

Daga Hussaini Yero, Funtua

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karɓi lambar yabo a karo na biyu daga ƙungiyar 'Peace Ambassadors Network' ta Nijeriya sakamakon ficen da ta yi wajan kula da walwalar Mata Da Marayu.

Hajiya Huriyya ta karɓi lambar yabon ne a wurin taron ya gudana a cibiyar Ƙungiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice da ke Abuja cikin makon da ya gabata.

Mataimakiya ta musamman akan yaɗa labarai ta Matar Gwamnan, Zahara'u Musa ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, ta miƙa a manema labarai a Gusau.

A cewar ta, jim kaɗan bayan  karɓar lambar yabon, Uwargidan Gwamnan, ta bayyana godiyar ta ga Allah Madaukakin Sarki da kuma waɗanda suka shirya taron da suka karrama ta a cikin wasu  fitattun ‘yan Nijeriya masu matuƙar daraja da kima.

Ta ce, "Na yi farin ciki da jin daɗi matuƙa bisa girmama ni da ku k ayi, da kuma kasancewa cikin waɗanda suka ci gajiyar waɗannan kyaututtuka.

"Zaɓata cikin waɗanda aka ba wannan Lambar karramawa a matsayina na mace mafi tsayuwa ga lamurran mata kan sha'anin daidaiton jinsi, abun jinjina ne da godiya Matuƙa.

“Na gode muku pwarai da gaske da kuka amince da irin gudumurwar da muke bayarwa kan  Sha'anin mata da yara."

Daga nan ne Uwargidan Gwamnan ta bayar da tabbacin ci gaba da ƙaddamar da shirye-shiryen ƙarfafa wa al'umma waɗanda ke da tasiri kai tsaye zuwa gare su.

Hajiya Huriyya Lawal ta kuma  bayyana mijinta Dauda Lawal a matsayin Jigo da ma'aunin dukkan nasarorin da ta samu.

A ƙarshe Hajiya Huriya Dauda ta sadaukar da kyautar karramawar ga al'ummar  jihar Zamfara baki ɗaya.

 

No comments