Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

ƘWACEN WAYA: Yadda Aka Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kashe Babban Soja A Kaduna

Sakamakon wani samame da gamayyar jami'an tsaro suka kai a wasu maboya miyagun matasa a Unguwar Kawo da ke Kaduna, an samu nasarar cafke...


Sakamakon wani samame da gamayyar jami'an tsaro suka kai a wasu maboya miyagun matasa a Unguwar Kawo da ke Kaduna, an samu nasarar cafke mutum 27, waɗanda ake zargi da kashe wani babban sojan ruwa, a yayin da suka ƙwace masa wayar salula.

Wannan samame ya zo ne 'yan kwanaki kaɗan bayan da sojan, Lt.-Cdr. Muhammad Buba ya samu matsalar fashewar tayar mota a gadar Kawo, ya tsaya don ya canja wata, amma wasu masu ƙwacen waya suka luma masa wuƙa, suka ƙwace wayar, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar sa. Abinnya faru da misalin ƙarfe 5:20 na asubahin ranar Lahadi.

Baya ga waɗannan miyagu da aka kama, jami'an tsaron sun kuma samu muggan makamai a tare da su, waɗanda suka haɗa da adduna, gariyo wuƙaƙe da kuma kayan shaye-shaye.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Mansur Hasan ya bayyana cewa bisa umurnin Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Rabiu Muhammad na cewa a gano maboyar waɗannan miyagun mutane tare da kamewa da tarwatsa su, rundunar, tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron farin kaya ta DSS, sojoji da  'yan ƙato da gora na jihar Kadjna KADVIS, sun kai samame a irin waɗannan wurare, inda suka kama waɗanda ake zargin, tare da muggan makamai.

Mansur Hasan ya ce, “A ranar 8 ga watan nan na Yuni 2025, da misalin ƙarfe 8:30nd, an gudanar da wani tsararren samamen haɗin gwiwa a yankin Kawo da maƙwabtanta. Sakamakon wannan samame, an samu nasarar kama mutum 27, inda kuma aka same su da muggan makamai.

“Abubuwan da aka samu a tare da waɗannan miyagu, sun haɗa da wuƙaƙe, adduna, gariyo da wani busasshe abu mai kama da ganyen wiwi, tare da wasu miyagun ƙwayoyi.

“Wannan yana nuni da irin jajicewar Kwamishinan 'yan sanda CP Rabiu Muhammad na tabbatar da tsaron lafiyar jama'a, tare da bin doka da oda a duk faɗin jihar Kaduna.

“Ya ce rundunar sa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bi ta kan duk wasu miyagu masu hana jama'a zaman. afiya."

Shi dai wannan babban jami'in sojan ruwa ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta zuwa kwalejin horas da manyan jami'an soji dake Jaji, inda ya samu matsalar fashewar tayar mota a gadar Kawo, inda ya tsaya don ya canja wata, a nan ne wannan mummunan abu ya faru.

No comments