Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DAMINAR BANA: Ministan Tsaro Ya Tabbatar Da Samar Da Tsaro Ga Manoma

Daga Hussaini Yero, Gusau Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Muhammed Matawalle ya tabbatar da samar da dakarun Tsaro na musamman da Jiragen sama ...


Daga Hussaini Yero, Gusau

Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Muhammed Matawalle ya tabbatar da samar da dakarun Tsaro na musamman da Jiragen sama don samar da tsaro ga Manoman ƙasar a daminar bana.

Ministan Matawalle ya bayyana haka ne a lakacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a gidansa da ke Maradun cikin Jihar Zamfara.

Matawalle ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya Æ™arÆ™ashin Jagorancin Shugaban Æ™asa ta shirya tsafa don samar da Dakarun Tsaro, da jiragen sama da za su shiga dazuka domin fatattakar 'Yan ta'adda a faÉ—in Æ™asar nan. "Don haka ina mai tabbatar wa Manoman Æ™asar nan, cewa  za su yi noma cikin aminci da tsaro da da yardar Allah," in ji Matawalle.

Kuma ya tabbatar da cewa hukumar tsaro na iyaka ƙoƙarinta wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ministan Matawalle ya kuma yaba wa wasu gwamnoni da suke taimakon Jami'an tsaron wajen yaƙi da 'Yan ta'adda a jihohin su. Ya kuma nuna takaicinsa ga wasu gwamnonin da suke ganin gazawar Jami'an tsaron a jihohin su, duk da ba su ba su gudumuwar da ta kamata na magance matsalar ba.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa, Shugaba Bula Ahmad Tinubu ya yi wa 'yan Arewa adalci a bangaren muƙamai da ya bada, musamman a gefen Tsaro na muƙamin Farar hula da masu kayan Sarki, duk 'yan Arewa ne ke Jagorancin su. Do haka 'yan Arewa babu abin da ya kamata su yi wa gwamnati Tinubu sai godiya da fatan alhairi.

Matawalle ya kuma yi kira ga al'ummar ƙasar nan da su ci gaba da yi mata addu'a don samun dawwamammen zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.
 

No comments