Daga Husaini Yero, Gusau Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya wa Makarantar Tsagayar da aka ƙaddamar a garin Gumi ta jihar sunan Sarki...
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya wa Makarantar Tsagayar da aka ƙaddamar a garin Gumi ta jihar sunan Sarkin musulmi Sultan Abubakar Sa'adu III, ya ce "wannan ne sunan Tsagayar da za a rinƙa kiran ta," in ji Gwamnan.
Gwamna Lawal ya furta haka ne a lokacin da ya ke gabatar jawabi wajen bikin ƙaddamar da Tsangayar, wanda ta na daga cikin ayyukan da ya ƙaddamar a cikin bukukuwan cikar sa shekara ɗaya a kan mulki.
Tun farko a nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa, "tun lokacin yaƙin nemam Zaɓe muka yi ma al'umma alƙawarin samar masu da Ilimi, wanda yanzu haka mun duƙufa wajen gyara makarantun da gina wasu sabbi a faɗin Jihar nan."
Don haka Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da cewa za su ɗauki nauyin Makarantar nan wajen kula da ita. Kuma irin wannan Tsangaya, guda uku ne muka yi a cikin wannan jiha, akwai a Gusau da Ƙauran Namoda, sai kuma wannan ta Gumi.
Shi kuwa a nasa jawabin ,Sultan Sa'adu Abubakar ya bayyana matuƙar jin daɗin sa, musamman ganin yadda gwamnatin Jihr Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ciri tuta wajen bunƙasa harkar Ilimin addini da na Zamani.
Ya ce, "Wannan Makaranta za ta taimaka gaya wajen samun ingantacen Ilimin addini da na zamani. Don haka Sultan Sa'adu Abubakar ya yi kira ga gwamnoni da su yi koyi da irin wannan shiri na Gwamna Dauda, musamman wajen bunƙasa Ilimin addini da na Zamani."
No comments