Jami'an Tsaro a Kano sun bayyana cewa binciken sirri ya nuna akwai wasu masu neman fakewa da dambarwar da ta dabaibaye naɗin Sarautar Ka...
Jami'an Tsaro a Kano sun bayyana cewa binciken sirri ya nuna akwai wasu masu neman fakewa da dambarwar da ta dabaibaye naɗin Sarautar Kano domin kawo tashin-tashina a jihar, wanda suka ce a shirye su ke wajen sanya ƙafar wanda ɗaya da duk wanda aka kama.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Husain Gumel ne ya bayyana haka a wani taron haɗin gwiwa da suka gabatar, wanda ya haɗa da 'yan sanda, sojoji, da jami'an farin kaya na DSS a Kano cikin makon nan.
Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa binciken su ya tattaro masu cewa waɗannan miyagun ɓata-gari sun shirya kai hari a Majalisar Dokoki, da wasu wurare a ƙwaryar birnin Kano.
Ya ce ko a waccan rana da ya ke magana, wasu matasa sun fara ƙona tayoyi a kan hanyar da ke zuwa fadar gwamnatin jihar.
Kwamishin ya yi ƙarin haske da cewa, akwai mutane da su ke ɗaukar nauyin waɗannan matasa, inda bincike ya nuna an biya gungun matasan Naira 150,000 kowannen su.
Saboda haka sai Kwamishinan ya bayyana cewa ba za su lamunci duk wani nau'i na tayar da zaune tsaye ba. Inda ya tabbatar da cewa akwai zaman lafiya a Kano, kuma mai ɗorewa.
Yana mai cewa aikin jami'an tsaro ne tabbatar da doka da oda, kuma ta ayyana duk wata maɓoya ta miyagun mutane a ƙwaryar Kano, za ta ɗauki tsattsauran mataki a kan su.
No comments