Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai bari Najeriya ta koma ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba a zamaninsa. Yayin da yake jawabi ga ...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai bari Najeriya ta koma ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba a zamaninsa.
Yayin da yake jawabi ga zaman haɗaka a Majalisar Tarayya a ranar Alhamis domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya kore raɗe-raɗin da ƴan jam’iyyun adawa ke yi na iƙirarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.
Yayin da yake bada amsa kan tsoron yan adawa na yadda ake tururwae dawowa jam’iyyar APC, Shugaba Tinubu ya ce jam’iyyar APC za ta aikata “babban kuskuren siyasa” idan ta hana ’yan jam’iyyun adawa shigowa cikin jam’iyyar.
Ya ce, “Nijeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba. Wannan ba zai faru ba. Amma za mu aikata laifin siyasa idan muka rufe ƙofofin ga waɗanda ke son shiga APC.”
Idan ba a manta ba, manyan yan adawar Gwamnatin Shugaba Tinubu sun cika kafafen yaɗa labarai da cewa ana ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya daya, lamarin da Gwamnatin ta bayyana a matsayin ruɗewar yan adawa duba da yadda suke rasa mabiya suna dawowa jam’iyyar APC.
A kwana-kwanan nan an samu dawowar Gwamnoni masu ci, Yan Majalisun Dokoki da Majalisar Dattawa daga sassa daban-daban na ƙasar zuwa Jam’iyyar APC daga wasu jam’iyyun adawa dake ƙasar.
No comments