Rundunar sojin Nijeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci a jihar Zamfara, bayan da dakarun Mobile Strike Team (MST)...
Rundunar sojin Nijeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci a jihar Zamfara, bayan da dakarun Mobile Strike Team (MST) na Operation FASAN YAMMA (OPFY) suka hallaka wasu fitattun ‘yan ta’adda a cikin wani sumame da suka kai a yankin Ƙunchin Kalgo, Ƙaramar Hukumar Tsafe, ranar Litinin 10 ga Yuni, 2025.
Cikin waɗanda aka kashe har da shahararren shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da AUTA, tare da abokan aikinsa Abdul Jamilu da Salisu, waɗanda suka daɗe suna sanya fargaba da tashe-tashen hankula a yankin.
Wasu manyan shugabannin 'yan bindiga guda biyu, ciki har da wanda aka tabbatar da sunansa da Babayé sun hallaka a yayin artabun. Hakazalika, dakarun sojin sun kashe Sale Ado Madele (wanda ake kira Sarki), ɗa na fari ga shahararren ɗan bindiga, Ado Alieru a wani harin na daban a Zamfara.
Dakarun Operation Fasan Yamma, sun kuma hallaka wasu ƙarin ’yan ta’adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke garin Danjibga, waɗanda ake zargin suna shirin kai hari bisa jagorancin wani da aka fi sani da Dogo Sule.
Wannan samame ya zama babban koma-baya ga ‘yan ta’adda da ke yunƙurin hana zaman lafiya a Zamfara da wasu sassa na Arewa maso Yamma. Rundunar sojin Nijeriya ta sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyar jama’a, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
No comments