Daga Ibrahim Muhammad, Kano A ƙoƙarinsa na tallafa wa 'yan jam'iyyar APC a jihar Kano daga tushe, ƙaramin Ministan gidaje Hon. Yusu...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
A ƙoƙarinsa na tallafa wa 'yan jam'iyyar APC a jihar Kano daga tushe, ƙaramin Ministan gidaje Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya raba wa tsofaffin shugabannin Ƙananan Hukumomi, mataimakansu da Kansiloli zababbu da masu gafaka na Ƙananan Hukumomin jijar 44, inda kuma wannan rabon ya bar baya da ƙura, wasu na ƙorafi.
An yi rabon tallafin ne a ranar Litinin a babban ɗakin taro na sakatariyar Gwamnatin tarayya da ke kan titin Katsina a Kano.
Sai dai rabon ya bar baya da ƙura sakamakon wasu daga tsofaffin Kansilolin da masu bada shawara sun koka da rashin samun tallafin bayan sun baro Ƙananan Hukumominsu na nesa.
Wasu Kansilolin sun shaida wa Matattarar Labarai cewa sun zo ne a matsayin wakilci na raguwar Kansilolin daga Ƙananan Hukumomin su, amma sai akace wani ya karbi nasu. Haka su ma masu bada shawarar an sami wannan matsalar na wasu sun karbi na wasu.
Wani tsohon shugaban Ƙansilolin da ya zo daga wata Ƙaramar Hukumar ya ce an soma rabon tallafi kuɗin cikin tsari, an bai wa shugabannin Ƙananan Hukumomi da na mataimakansu a cikin tsari na yanayi mai kyau, amma daga baya da aka zo kan na Kansiloli ne tsarin ya karye, abin da wasu ke ganin kamar da gangan aka yi domin a rikita tsarin.
Sai dai bayan jan lokaci ana tinja-tinja na yadda za a bada kuɗin tun daga ɗakin da ake taron sai da aka fito waje aka kusa zagaye harabar bene na ɗaya da aka yi taron don ganin yadda za a shawo kan lamarin da a ƙarshe aka zartar da biyan kowane mutum da ya zo wajen.
Sai dai wani tsohon Kansila da shi ma ya zo a matsayin wakilci, zai karbi na tsofaffin Kansilolin yankin su, ya ce shi bai karba ba, abin da ya sa kuma bai karbi kudin ba, ya je taron ne a wakilcin tsofaffin Kansilloli na yankinsu, amma sai aka ce shi kaɗai za a ba, dan haka bai karba ba.
Mun yi ƙoƙarin ji daga masu ruwa da tsaki na rabon tallafin da suka hada da tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, tsohon dan majalisar jiha na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da tsohon shugaban Ƙaramar hukumar Fagge Hon. Ibrahim Abdullahi Shehi wanda suna daga cikin manyan hadiman Ministan, amma ba wanda ya amince muka yi magana da shi.
Sai wani daga cikin tawagar masu rabon a gefe ya shaida mana cewa rabon da kyakkyawan manufa aka yi shi, da kuma tsarin da kowa zai samu amma sai aka sami karyewar tsarin, amma duk wanda sunansa ke cikin jerin sunayen tsofaffin kansilolin da masu bada shawara da shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu na Gwamnatin APC da ta gabata za su samu, ba wanda zai rasa.
A yayin taron shugaban Ata social media da Maliya "media reporter "na karamar hukumar Gabasawa daga Kano ta Arewa Buhari Muhammad Karmami ya karrama Ministan da Sanata Barau I Jibrin.
Ya ce sun karrama karamin ministan gidajen Hon. Yusuf Abdullahi Ata ne saboda tun da ake ministoci daga Kano ba a sami kamar sa a wajen taimakon jama'a ba.
Ya ce Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya riƙe ma'aikatar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ba shi na karamin ministan gidaje da kulawa da yin aiki tuƙuru yana habaka ci gabanta.
Muhammad Karami ya ce shi ma mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin yana kawo ci gaba sosai a harkar ci gaban ilimi da tallafa wa matasa da kuma ganin an bunƙasa ci gaban Arewa maso Yamma.
No comments