Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An sami Gagarumin Ci Gaba A Shekara Ɗaya Na Mulki Gwamnatin Abba Kabir -Salisu Ahmad

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu na Jihar Kano, Farfefesa Salisu Ahmad Ibrahim ya bayy...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu na Jihar Kano, Farfefesa Salisu Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a shekara ɗaya na mulkin Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, duk kuwa da ɗimbin ƙalubalen da suka addabi gwamnatin, musamma na shari'a da tsarin mulki.

Farfesa Salisu ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da wakilin mu cikin makon nan, inda ya ce idan aka dubi ɓangaren tsaro ya ingant, domin kafin zuwan Gwamnan Abba babu yadda za a yi mutum ya ɗaga waya akan hanya ba tare da tararradadi ln za a iya fito maka da makami a ƙwace ba. Amma yanzu ko'ina mutum zai ɗaga waya ya yi, ba tare da tsoro ba.

Ya ƙara da cewa, "sannnan a cikin watan Azumin da ya gabata, Gwamna Abba ya ciyar da bayin Alla, wanda har ɓangaren Gwamnatin tarayya da Dangote sun taimaka da abinci da aka raba wa mutane.

Haka kuma, an kyautata walwalla da jin daɗin jama'a ta hanyoyi da dama. Sannan Gwamna ya ƙaddamar da tsarin tallafa wa Mata guda 200 a Ƙananan Hukumomi na birni da guda 100, a ragowar Ƙananan Hukumomi ana ba su  jari na N50,000, wanda hakan ba ƙaramin taimaka wa haɓaka tattalin arziki zai yi ba."

Furofesa Salisu ya ce idan aka dubi ɓangaren kula da lafiya, Gwamnan ya bada kulawa wajen gyara Asibitoci da dam. A Asibitin Murtala an gyara ɓangaren karɓar marasa lafiya na gaggawa, haka a Asibitin Nasarawa da na Muhammad Sanusi, su ma an gyara su, da Asibitoci na Matakin farko an gyara, sannan an karɓo Asibitin yara da aka sayar na Asiya Bayero, an gyara ana kula da lafiyar yara da bayar da magunguna kyauta. 

Ya ƙara da cewa an inganta harkar yin rigakafin cututtuka, "domin ko a lokacin da Gwamna ya zo, ciwon mashaƙo ya ta'azza a jihar, amma da taiimkon Gwamnatin tarayya an daƙile bazuwar cutar. Haka duk wani nau'in rigakafi da gwamnatin baya ta yi biris da shi, yanzu an dawo da shi an sami nasara cikakke akai.

Da ya ke ƙarin haske gane da nasarar da ya samu a Hukumar da ya ke jagoranta kuwa, Faufesa Salisu Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa an samu nasarori da dama, wanda babbar ita ce na sama musu wajen zama na kansu saɓanin baya, sannan da ba su kuɗaɗen gudanarwa akan lokaci,  ga kuma gyara dokokinsu da aka yi daidai da zamani don inganta harkar lafiya. 

Sannan ya ce sun buɗe ofis na musamman na masu maganin gargajiya, sun soma ɗaukar ƙididdigar adadinsu a Kano, da irin gudumawar da suke bayarwa. Za a rinƙa ba su takardar shaida don tsaftace ayyukansu.

Ferfesa Salisu Ahmad Ibrahim ya yi nuni da cewa koyaushe Gwamna yana da kyakkyawar zuciya na son ya  gyara jiharKano, ya yi alƙawura, a koyaushe ka same shi zai yi ta cewa a taya shi da addu'a ya sauke nauyin da kw kan sa na alƙawura da ya yi wa mutane.

Don haka Farfesan ya yi kira ga jama'a su riƙa sa wannnan Gwamnati a addu'a, Àllah ya ba ta ikon sauke nauyin da ke wuyar ta na jagoranci jihar Kano.

 

No comments