Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar CRC Ta Jihar Kano Ta Na Tallafa Wa Ci Gaban Al'umma -Hon. Shakur Abdulyassar

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Hukumar kyautata ɗa'a ta Jihar Kano (CRC) ta cimma nasarar aiwatar da cika muhimman  alƙawuran da Gwamna Alh...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Hukumar kyautata ɗa'a ta Jihar Kano (CRC) ta cimma nasarar aiwatar da cika muhimman  alƙawuran da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf  ya yi na talla wa al'umma  a ƙarƙashin ta.

Shugaban hukumar, Hon.Shakur Abdulyassar ne ya bayyanna haka lokacin da ya ke zantawa da 'yan jarida game da cika shekara ɗaya na Gwamnatin Kano akan mulki. Ya ce, ko wata ɗaya ba a yi ba da rantsar da Abba ya sahalle wa hukumar ta soma raba tallafin Awaki da Takin noma da sauran abubuwa da dama.

Ya ƙara da cewa, kullum Gwamna yana ƙirƙiro ayyukan da za su taimaka wa jama'a a ƙarƙashin wannan hukumar ta ( CRC ). Ya ce, ko a cikin watan Mayun nan an bayar da N50,000 ga kowace mace, kuma waɗanda suka amfana sun kai guda 5,000, sannan haka za a ci gaba   da ɗorawa ana yi.

Shugaban ya ce, kowane lokaci ana tallafa wa mata da matasa da masu buƙata ta musamman daban-daban, kama daga makafi, guragu da kutare. 

"Ko a kwanannan, Uwargidan shugaban ƙasa da uwargidan Gwamna ta wakilce ta, ta ƙaddamar da  bayarda N50,000 ga kowace mace, domin su je su yi aikin noma a Ƙaraman Hukumomi  44 na jihar nan. Sannan an  raba kayan abinci, babu inda ba su amfana ba," in ji shi.

Daga nan shugaban na Hukumad CRC ya  jaddada  godiya ga Allah da ya kawo wannan Gwamnati ta Abba Kabir da ta zama abin alfahari ga duk ɗan Kano, talakawa na taƙama da ita.

Hon.Shakur Abdulyassar ya ce  yanzu Gwamna yana gudanar da aiki, waɗanda su ka yi cuta da ha'intar al'umma ana dawo da komai kan turba, waɗanda suka zalunci Kano suka sayar da filin sallar Idi da ginen makarantu da irin su filin sukuwa da aka baiwa 'ya'yan manya,  suka tsaga maƙabartu suka saya, yanzu an ƙwato su an dawo da su ga al'umma. 

A ƙarshe Hon. Shakur Abdulyassar ya ja hankalin al'ummar Kano akan su ci gaba da yi wa Gwamna Abba addu'ar Àllah ya ba shi nasara da galaba akan maƙiya, ya ba shi ikon yi wa Kano hidima a koyaushe.

 

No comments