Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RAHOTON MUSAMMAN: Har Yanzu Al'ummar Tudun Biri Ba Su Ga Diyya Ko Tallafi Ba

Rahotanni na nuni da cewa, watanni huɗu ke nan bayan mummunan harin bom ɗin nan da sojoji suka kai, wanda ya laƙume rayuka sama da 100 daga ...


Rahotanni na nuni da cewa, watanni huɗu ke nan bayan mummunan harin bom ɗin nan da sojoji suka kai, wanda ya laƙume rayuka sama da 100 daga wasu al’ummomi uku a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce har yanzu suna jiran a biya su diyya na asarar da suka yi.

Wannan jefa bom, wanda ya faru a ranar Lahadi 3 ga watan Disamba, 2023, ya yi sanadiyar salwantar rayuka da raunata jama’a a garuruwan Tudun Biri, Ugara da Sabon Gida bayan da suka taru a Tudun Biri domin murnar Mauludi.

Musa Umar, wanda ya rasa 'ya’ya shida a wannan mummunan lamari, ya zauna shiru a gidansa da babu kowa sai shi. Ya kan shiga tunani mai zurfi, yana tunawa da ranar da aka hallaka dukan iyalinsa ta hanyar harin jirgi mara matuƙi.

Rana ce da ya bayyana a matsayin iftila'i da ya afka wa iyalansa da wani ƙaramin ƙauye dak e bayan filin jirgin sama na Kaduna. Ya bayyana cikin nutsuwa amma yana jin zafi a duk lokacin da ya tuna cewa a baya gidansa cike yake da yara suna wasa amma yanzu babu kowa, domin duk ’ya’yansa shida sun mutu a harin.

“Har yanzu ina cikin jin raxaxin zafi a duk lokacin da na tuna rasa ’ya’yana shida a faɗowar bom ɗaya. Bayan faruwar lamarin, da kyar na yi barci saboda na kan tashi da daddare ina kuka ni kaɗai a ɗaki,” inji shi.

Manomin ya ce, ’ya’yansa da suka rasu sun kasance farin cikinsa a lokacin da suke raye, inda ya ce yanzu farin cikin ya ƙare amma Allah yana ƙara masa haƙuri da sauran waɗanda suka rasa ’yan uwansu a ƙauyen. A cewarsa, mummunan lamarin da ya faru a ranar 3 ga Disamba 2023 zai kasance tare da shi har sai ya koma ga Allah, saboda ba zai iya mantawa ba.

“Ba zan taɓa mantawa da abin da ya faru a ranar ba saboda waɗannan yara ne da nake fatan za su kula da ni a nan gaba, amma duk an kashe su a rana guda. Amma duk da haka ina godiya ga mahaliccina domin shi ne ya fi kowa sanin dalilin faruwar haka,” ya fafa yana shassheƙar kuka.

Matattarar Labarai ta ruwaito yadda jiragen yaƙin sojoji suka kai wa mutanen ƙauyen hari a bisa kuskure a lokacin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi.

Wannan mummunan harin dai ya janyo tofin Allah tsine daga ciki da wajen ƙasar, inda shugabannin sojoji suka ɗauki alhakin lamarin.

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta yi alƙawarin sake gina ƙauyen tare da biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa.

Don haka mutane da dama da suka haɗa da ’yan majalisar dokokin ƙasar sun ziyarci jihar domin jajanta wa jama’a tare da yin alƙawarin taimakawa waɗanda abin ya shafa.

An tattaro cewa har yanzu ba a biya waɗanda abin ya shafa diyya ba, watanni huɗu bayan faruwar lamarin. Haka kuma har yanzu ba a sake gina al’ummar ta hanyar shirin Fulako na Gwamnatin Tarayya kamar yadda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi alƙawari lokacin da ya ziyarci jihar a madadin shugaban ƙasa ba.

Shi ma Jafar Abdullahi, wani mazaunin yankin, ya ce a matsayinsu na Musulmi, sun yi imanin abin da ya faru ya faru da su ne bisa ƙaddarar Allah Mahalicci.

Ya bayyana cewa wani vangare na alƙawarin da gwamnati ta yi shi ne samar da gidaje ga mazauna garin amma tun bayan faruwar lamarin, ba su samu gida ko ɗaya ba.

Abdullahi ya ce, a kwanan baya, gwamnati ta sake ziyartar al’umma a ranar 26 ga Maris domin ƙaddamar da aikin gina titin kilomita 5.25, asibiti da cibiyar koyar da sana’o’i a ƙauyen.

"Eh, an samar da ruwa a cikin al'umma kuma ana gina masallaci amma har yanzu muna jiran sauran alqawuran da aka yi mana," inji shi.

Dangane da batun biyan diyya, ya ce, “Sun yi alƙawarin biyan diyya kuma har yanzu muna fatan za su biya amma idan ba su yi ba, Allah yana kallo tunda ba za mu iya yaqar gwamnati ba. Amma idan sun biya, muka ce ba su biya ba, Allah yana kallonmu,” inji shi.

Ya bayyana cewa galibin ’yan kuɗaɗen da waɗanda abin ya shafa suka samu daga masu hannu da shuni ne da suka ziyarce su a asibiti.

An tattaro cewa masallacin zai kasance masallacin Juma’a na farko a cikin al’umma idan an kammala shi kuma wani babban jami’in gwamnati a Abuja ne ke gina shi a wani ɓangare na taimakonsa ga al’ummar ƙauyen.

Haka kuma an samar da sabuwar rijiyar burtsatse domin sauƙaƙa musu matsalar ruwa, daga nan aka ƙaddamar da hanyar da za ta haɗa ƙauyen da titin filin jirgin sama, cibiyar kula da lafiya a matakin farko, da kuma cibiyar koyon sana’o’i da gwamnatin jihar za ta yi a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na sake gina ƙauyen.

Wani shugaban al’umma wanda kuma mamba ne a kwamitin sa-ido kan biyan diyyar Malam Muhammad Bello Buruku ya bayyana fatan gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka ga waɗanda lamarin ya shafa.

Ya kuma tabbatar da cewa tuni kwamitin ya gana domin shirya yadda za a raba kuɗaɗen ga hannun waɗanda abin ya shafa.

Ya ce duk da cewa akwai wasu mutanen da suka yi alƙawarin kuɗi amma har yanzu ba su karɓi irin waɗannan alƙawuran ba.

Ya ce a halin yanzu akwai wasu kuɗaɗe da za a raba wa waɗanda suka rasa ’yan uwansu, waɗanda suka samu munanan raunuka da kuma wasu da suka samu ƙananan raunuka.

"Muna fatan nan ba da jimawa ba za a biya wa kowa diyya na asarar da ya yi," inji shi.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka, ya kuma buƙaci jama’a da su cigaba da haƙuri da gwamnati, yana mai cewa za a yi masu adalci.

Da aka tuntuɓi Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu ya tabbatar da cewa akwai alƙawuran da ba a biya ba, amma ya ce tuni Gwamna Uba Sani ya fara gina titin kwalta mai tsawon kilomita 5.25 daga filin jirgin Kaduna zuwa Tudun Biri; asibiti da cibiyar koyon fasaha.

No comments