Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Me Ya Sa EFCC Ke Neman Yahaya Bello Ruwa-a-jallo?

Hukumar yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana cewa Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya shiga cikin jerin sunayen w...

Hukumar yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana cewa Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya shiga cikin jerin sunayen waɗanda ta ke nema ruwa-a-jallo.

Matakin hukumar na zuwa ne 'yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da Hukumar ta shigar saboda wanda ta ke zargin bai halarci zaman kotun ba.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis ɗin nan, Lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa "wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa Tsohon Gwamnan mafaka".

Hukumar ta ce, "EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin sace kuɗin haram da suka kai Naira Biliyan 8.2."

Tun a ranar Laraba rahotonni suka nuna cewa gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami'an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

Ya zuwa haɗa labarin nan dai Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin.

Lauyan hukumar ya kuma ce suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar sojin Nijeriya wajen kamawa tare da gurfanar da shi a gaban kotun.

In dai za a iya tunawa, a jiya Labara ne jami'an Hukumar ta EFCC suka yi wa gidan Tsohon Gwamnan da ke Abuja ƙawanya don cafke shi, amma kafin su kai ga kama shi, sai Gwamnan jihar Kogin, Ododo ya dira gidan, wanda daga bisani ya sulale sa shi. 

 

No comments