Mutane uku ne suka mutu yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka bayan da wata motar sintiri ta sojojin Nijeriya ta buge...
Mutane uku ne suka mutu yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka bayan da wata motar sintiri ta sojojin Nijeriya ta buge wani mai adaidaita sahu, lamarin da ya yi sanadin jikkata direban da fasinjojinsa.
Wani ganau mai suna Adamu Hassan ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a babbar kasuwar Garin Alkali ta Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar Bade ta jihar.
“Bayan faruwar lamarin ne Æ™ungiyar ’yan adaidai sahu suka gudanar da zanga-zanga a wasu wuraren da suka tare babban titin zuwa Gashua, hedikwatar Æ™aramar hukumar Bade.
“Jami’an sojojin da suka fusata sun dawo suka fara harbi ba Æ™aƙƙautawa, abin takaici wasu masu zanga-zangar sun ji rauni kuma daga baya aka kwashe su zuwa Asibitin kwararru, Gashua domin kula da lafiyarsu,” inji shi.
Wata majiya daga Asibitin Kwararru Gashua ta ce an shigo da waÉ—anda suka jikkata da dama ciki har da gawarwaki a asibitin, amma ba a iya tantance adadinsu ba.
No comments