Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cewa tana ƙoƙari wajen sauke nauyin al'ummar Jihar Kano a ɓangaro...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cewa tana ƙoƙari wajen sauke nauyin al'ummar Jihar Kano a ɓangarori da dama da suka haɗa da inganta ilimi da lafiya da da ci gaban matasa da sauran fannoni da dama.
Mataimakin shugaban ƙungiyar 'Yan Tifa ta ƙasa, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar na jihar Kano, Kwamared Mamunu Ibrahim Takai ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ,'yan jarida a Kano cikin makon nan.
Kwamared Mamunu Ibrahim Takai ya kuma yaba da irin ayyuka da ɗan Majalisar tarayya Mai wakiltar Takai da Sumaila , Barista Rabiu Yusuf yake yi domin bunƙasa ci gaban al'umma, musamman yadda ya riƙe kowa da kyautata wa ci gaban yankin.
Ya yaba wa jagoran Kwankwasiyya na Takai, tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Takai, tsohon Kwamishina, tsohon ɗan Majalisa, mai baiwa Gwamnan Jihar Kano shawara akan harkokin Ƙananan Hukumomi, Hon Garba Umar Durbunde bisa irin ƙoƙarin da ya ke wajen ganin ci gaban al'ummar Takai.
Kwamared Mamunu Ibrahim Takai, wanda jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya da ke neman tsayawa takarar shugaban Ƙaramar Hukumar, ya ce Ƙaramar Hukumar Takai na son ta sami shugaba da zai kawo sauyi domin bunƙasa ci gaban ta saƙo da lunguna domin kyautata jin daɗin al'umma.
Ya ce, shekaru da yawa yana cikin harkar siyasa ƙarƙashin tsarin na yarda da manufofin Kwankwasiyya sun yi aiki sosai wajen shiga da fice domin tabbatar da samun nasarar jam'iyyar NNPP tun daga zaɓen shugaban ƙasa da na Sanatoci da Majalisar tarayya da na Gwamna da Majalisar jiha a 2023.
Ya ce Ƙananan Hukumomi, musamman irin nasu na karkara na cikin wani yanayi, shi da kansa ya shiga lungu da saƙo na Ƙaramar Hukumar su ta Takai, mazaɓu daban-daban tun daga mazaɓar Takai, Kachako, Zuga, Falali, Kuka, Karfi da sauran mazaɓun babu inda ba su shiga ba domin su ga cewa sun isar da saƙon na manufofin Kwankwasiyya da neman nasarar NNPP.
Mamunu Ibrahim Takai ya ce yana da kyakkyawan niyya da manufofi masu kyau na kawo ci gaban yankin cikin yardar Allah.
Ya ce, ko yanzu da ya amince zai tsaya neman takarar Shugabancin, wanda mutanen Takai suka nemi ya fito, ya sami karɓuwa daga al'umma da jagororin su na siyasa na Takai, dukkansu ana cikin mutunci da girmamawa sun yarda su iyaye ne sun riƙe su a matsayin 'ya'ya.
Ya ce, za su tabbatar da sun yi abin da ya dace wajen bunƙasa ci gaban jama'a da gina ilimi da lafiya da matasa, wanda wannan shi ne tsari na Madugun Kwankwasiyya da za su yi ƙoƙari su aiwatar in sun sami dama, su fitar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf kunya, ta baiwa manufofin gwamnatin sa na gina ci gaban al'umma goyon baya.
A ƙarshe Kwamared Mamunu Ibrahim Takai ya yi fatan sabon shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Takai, Hon. Abdulhadi Falali da Mataimakin sa Hon. Muhammad Abdullahi da Sakataren Ƙaramar Hukumar, Hon. Husaini Gambo da sauran Kansiloli, Allah zai musu jangora wajen gudanar da ayyuka na bunƙasa ci gaban yankin a wannan dama na shugabancin riƙo da aka ba su.
No comments