Daga Musa Muhammad Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatin sa ba ta ci bashin ko sisi ba, a waÉ—annan watanni tara da...
Daga Musa Muhammad
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatin sa ba ta ci bashin ko sisi ba, a waÉ—annan watanni tara da ya hau mulki, duk da É—imbin bashin da ya gada daga gwamnatin da ta shuÉ—e ta Nasiru El-Rufai.
“Mun yi nazari cikin tsanaki kan halin da muke ciki. Ina sanar da ku cewa duk da É—imbin bashin da muka gada, har zuwa yanzu ba mu ciyo bashin ko kwabo ba,” in ji shi.
Gwamna Uba Sani ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya Asabar yayin da yake jawabi a wajen wani babban taron ji daga jama'a, inda ya ce ɗimbin bashin da ake bin jihar Kaduna shi ke laƙume ɗan abin da ta ke samu.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji bashin DalarAmurka Miliyan 587 da bashin Naira Biliyan 85 da kuma ayyukan kwangila 115 daga gwamnatin Nasir El-Rufai.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira Biliyan 7 daga cikin Naira Billiyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata a watan Maris, domin biyan bashi.
Gwamnan ya kuma koka kan tashin farashin canji, wanda ya ce jihar na biyan kusan ninki uku na bashin da gwamnatin baya ta karɓo.
Ya Kuma koka da yadda gwamnatin El-Rufai ta bar wa jihar Biliyan uku kacal a asusun, wanda ya gaza biyan albashin ma’aikata da ake biya na Naira Biliyan 5.2 a duk wata.
Gwamnan ya Æ™ara da cewa muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba sun haÉ—a da tsaro, samar da gidaje, ilimi, kiwon lafiya da tallafa wa masu Æ™ananan sana’o’i.
Ya ce gwamnatin sa za ta kuma mayar da hankali wajen samar da ci gaba ta hanyar saka hannun jari, inganta tattalin arziki da samar da gidaje masu sauki.
Ya ka bayyana wasu muhimman abubuwan da gwamnatin tasa ta sa a gaba a 2024 da suka haɗa da tsaro, samar da ababen more rayuwa, bunƙasa ilimi, samar da gidaje da ci gaban birane da dai sauransu.
No comments