Daga Musa Muhammad Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙira ga shugabannin addini da sauran masu mutunci a ƙasar nan, da su daina tsine...
Daga Musa Muhammad
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙira ga shugabannin addini da sauran masu mutunci a ƙasar nan, da su daina tsine wa Nijeriya a tarukansu ko wuraren wa’azi, kamata ya yi su a rinƙa yi mata addu'ar fatan alhairi da ci gaba.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a Fadar sa da ke Abuja a ranar Alhamis, yayin ya ke jawabi wajen taron buɗa-baki, wanda ya shirya wa Malaman addinai da masu Sarautun gargajiya.
Shugaban ya ce, “A ranar Laraba na halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Okuama, Jihar Delta. Na ga matansu masu ciki da yara ƙanana.
”Soyayyar al’umma tana hannunku. Ku yi wa ƙasar mu addu’a, ku bai wa yaran mu ilimi da tarbiyya. Wa’azin da muke yi wa mutane a coci da masallatai suna da muhimmanci, don haka mu rinƙa faɗa masu abubuwan da za su ciyar da ƙasa gaba, ba wai munanan kalamai ba.
“Kada ku la’anci al’ummar ku. Wannan ita ce ƙasar ku; kar a yi Allah-wadai da ita a cikin wa’azi, kada ku zagi ƙasar nan. Shugabanci na nufin kawo sauyi.
“A ce wannan shugaban ba shi da kirki, wannan ba laifi ba ne, amma ku bari sai zaɓe na gaba sai ku sauya shi, amma ku daina la’antar ƙasar nan. Kar ku zagi Nijeriya. Wannan kyakkyawar ƙasa ce.”
Daga nan sai Shugaba Tinubu ya jawo hankalin su wajen muhimmancin sauya aƙidun mutane, ta hanyar cusa musu kishin ƙasa da ɗora su a hanya mafi dacewa.
Shugaban ya buƙaci shugabannin addinai da suka kasance masu adalci wajen sukar masu riƙe da muƙaman siyasa.
Haka kuma Tinubu ya jadadda wa shugabannin aniyarsa ta magance ɗimbin matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan nan.
Wannan taron buɗa-bakin dai ya samu halartar Sarakunan gargajiya daga Arewaci da Kudancin Nijeriya da kuma Malaman addinin Musulunci da na Kirista.
No comments