Daga Musa Muhammad Ga dukkan alamu dai an fara samun rabuwar kai a fagen siyasar Jihar Kaduna tun da Gwamna Uba Sani ya bayyana adadin tulin...
Daga Musa Muhammad
Ga dukkan alamu dai an fara samun rabuwar kai a fagen siyasar Jihar Kaduna tun da Gwamna Uba Sani ya bayyana adadin tulin bashin da gwamnatin da ta shuÉ—e ta Malam Nasiru El-Rufai ta bar masa.
Domin, Jim kaÉ—an bayan Gwamna Ua Sani ya yi wannan magana ta bashin ne sai aka ga É—an Tsohon Gwamnan, Bashir El-Rufai ya maida martani a shafin sa na X, inda ya ce rashin iya mulki ne kawai ke damun su, amma ba wai yawan bashi ba ne.
Bashir El-Rufai ya riƙa yin wasu shaguɓe da ake zargi gwamnatin Uba Sani yake mayar wa martani mai zafi.
A ƙoƙarin sa na kare gwamnatin baya, wacce mahaifin sa ya jagoranta, Bashir ya nuna cin bashi ba laifi ba ne, domin ko jihar Legas ma ta na da bashi.
Ya ce: "waɗannan mutane sun fahimci ba su iya komai ba, da sunan mulki, ahi ne su ke neman yadda za su ɓoye wannan shirme da sakin layi."
"Tun daga Gwamnan, wanda a kullum bai da aiki sai na maƙalewa a Abuja, har zuwa tulin tarkacen hadiman da ya naɗa saboda sakaryar manufar siyasa kurum, amma ba su iya komai ba," in ji Bashir El-Rufai.
ÆŠan Tsohon Gwamnan ya janyo abin magana a shafin nasa da ya ce ana kashe Naira Biliyan 7 a wurin gina É—akin taro a daidai lokacin da ake kukan babu kuÉ—i.
"Gwamnati mai-ci a Kaduna tana gina É—akin taron N7bn kuma ta na kukan bashin da tsohuwar gwamnati ta bar mata," in ji Bashir El-Rufai.
No comments