Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Sa Ƙafar Wando Ɗaya Da Masu Ambato Juyin Mulki A Ƙasar Nan — Sojoji

  Daga Sulaiman Umar Rundunar Sojin Nijeriya ta gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da a...

 

Daga Sulaiman Umar

Rundunar Sojin Nijeriya ta gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin ƙasar nan.

Nijeriya dai na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abin da ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan ƙasar nan, inda

wasu daga cikin al'ummar kasar su ke ta kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu, tare da karɓe iko kamar yadda aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Sai dai Daraktan Tsaro na Sojin Nijeriya, Janar Christoper Musa, ya ce masu wannan kiraye-kiraye ba sa nufin ƙasar da alkahairi.

Don haka sai ya ce, dakarun sojin Nijeriya za su sa ƙafar wando ɗaya da masu wannan kiraye-kiraye.

Ya ce, abin da sojoji za su yi a yanzu shi ne kawai duba hanyoyin samar da sauƙin rayuwa da kuma ciyar da ƙasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba.

Da yake amincewa da halin matsi da ’yan Nijeriya ke ciki, Janar Musa, ya ce babu inda juyin mulki ke zama alkahairi a duniya. Don haka su ba za su yi wa Nijeriya fatan ci bayan da yake biyo bayan juyin mulki ba.

Daga nan Janar Musa ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri da fatan alhairi bisa halin da ƙasar ke ciki.

Har wa yau, ya buƙace su da su kasance masu juriya don cin moriyar tsare-tsaren da gwamnati ke bijirowa da su a nan gaba.

No comments