Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsanancin Ƙarancin Abinci Zai Ta’azzara Mutuwar Kananan Yara A Gaza – MDD

Daga Sulaiman Umar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, akwai yiwuwar matsanancin ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki da sabbaba cutuka...

Daga Sulaiman Umar

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, akwai yiwuwar matsanancin ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki da sabbaba cutukan ka iya haifar da ƙaruwar mutuwar ƙananan yara a Zirin Gaza.

Mako 20 da fara wannan yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas a yankin Zirin Gaza, Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi kashedin cewa, akwai matsanancin ƙarancin abinci da tsaftataccen ruwa a yankin na Falasdinawa, inda suka ƙara da cewa akasarin ƙananan yara sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Mataimakin Shugaban Ayyukan jin-ƙai na Assusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Mista Ted Chaiban ya ce, Zirin Gaza zai fuskanci mutuwar ƙananan yara, wanda zai ta’azzara halin da ake ciki a yanzu.

Wani nazari na haɗin gwiwa da Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi na nuni da cewa, kashi 90 na ƙananan yara daga shekara 5 zuwa ƙasa a Gaza sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Harin da mayaƙan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum dubu 1 da 160 ne ya haddasa yaƙin Gaza. Mahukuntan Zirin Gaza sun ce, hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum dubu 29 a halin da ake ciki.

Tun da aka fara wannan yaƙi, Zirin Gaza ya faɗa cikin matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, sakamakon yadda aka taƙaita shiga.

 

No comments