Jami'an 'yan sanda a jihar Neja sun samu wasu bindigogi ƙirar AK-47 har guda 350 a wani gidan kaji da ke hanyar Sabon Wuse-Garam a Ƙ...
Jami'an 'yan sanda a jihar Neja sun samu wasu bindigogi ƙirar AK-47 har guda 350 a wani gidan kaji da ke hanyar Sabon Wuse-Garam a Ƙaramar Hukumar Tafa ta jihar, inda suka kame mutum 4 masu alaƙa da wurin.
Ita dai wannan hanya ta Sabon-Wuse-Garam, ita ce ta haɗe har zuwa Bwari da ke ƙarƙashin babban birnin tarayya, Abuja, wanda shi ma ake samun yawan sace-sacen mutane a yankin.
Rahotanni na nuni da cewa wani mai bayar da rahotannin sirri ya bayyana cewa cikin waɗanda aka kama har da Manajan gonar, wasu ma'aikatan gonar su biyu da wani da ya kai ziyara.
Ya zuwa haɗa rahoton nan dai ba mu sami ta bakin Kakakin rundunar ta jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ba.
No comments