Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Nijeriya (AMBCN) ta bayyana cewa ta janye yajin aikin da ta shiga, inda ta janyewar ta biyo bayan wata tatta...
Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Nijeriya (AMBCN) ta bayyana cewa ta janye yajin aikin da ta shiga, inda ta janyewar ta biyo bayan wata tattaunawa ce da suka yi da jami'an ma'aikatar noma ta ƙasa.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, a cikin wata sanarwa ƙungiyar burodin ta fitar da yammacin jiya Laraba, wacce ta samu sa hannun shugabanta, Mansur Umar, ta ce ta cimma wasu yarjeniyoyi da gwamnatin tarayya a tattaunawar tasu, wanda hakan ya sanya ta sanar da janye yajin aikin da ta fara a ranar Talata.
Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati sun haɗa da fitar da metric tan 25,000 na alkama nan take ga kamfanonin fulawa domin sarrafawa da samar wa masu sana'ar burodi.
Haka nan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kan sake duba shirin samar da fulawa daga rogo da dankali da kuma dawa.
Sannan kuma an cimma yarjejeniyar tallafa wa masu sana'ar ta burodi ƙarƙashin wani shiri na ma'aikatar noma.
Masu gidajen burodin a Nijeriya dai sun shiga yajin aiki ne bayan kokawa da tsadar farashin kayan aiki, lamarin da ke kawo tarnaƙi a harkar sana'ar tasu.
No comments