Kamfanin sadarwa MTN a Nijeriya ya nemi afuwar aboka hulɗarsa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar, musam...
Kamfanin sadarwa MTN a Nijeriya ya nemi afuwar aboka hulɗarsa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar, musamman a jiya Laraba.
Tun da tsakar ranar Laraba ne dai masu amfani da layin MTN suka fara fuskantar matsalar ɗaukewar sabis a layukansu.
Sai dai kamfanin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce hakan ta faru ne sakamakon yankewar wasu wayoyin sadarwar kamfanin, wanda lamarin ya shafi kira da kuma fannin intanet a layin.
Kamfanin ya kuma ce injiniyoyinsa na aiki domin shawo kan matsalar, inda ya ce sannu a hankali sabis ɗin ya fara dawowa a wasu yankuna.
No comments