Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da hamshaƙan ’yan kasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tatt...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da hamshaƙan ’yan kasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma tsadar rayuwar da ’yan ƙasar ke fuskanta.
Taron ya kuma tattauna kan yadda darajar kuɗin kasar, Naira ke faɗuwa yayin da darajar dalar Amurka ke ƙara tashi, a yayin ganawar ta ranar Lahadi.
Baya ga batun tattalin arziki taron ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi wadata ƙasar da abinci da kuma na tsaro.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, "kamar yadda na sha faɗa al’ummar kasar nan su ne kaɗai mu ke da su, kuma muke son kyautatawa, mun damu matuƙa da halin da suke ciki"
Cikin waɗanda suka halarci taron a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, sun haɗa da attajirin ɗan kasuwar Nijeriya Alhaji Aliko Dangote.
"Mun tattauna kan batun samar da ayyukan yi da wasu batutuwa da dama... abin alfaharin shi ne Najeriya ƙasa ce mai albarka, kuma mu na da kyakkayawan fata kan za mu iya sauya tattalin arzikinmu kuma za mu tabbatar da hakan," inji Dangote.
No comments