A wani ƙazamin rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Jihar Zamfara, ƙungiyar Ado Allero ta kashe aƙalla fitattun shugabannin...
A wani ƙazamin rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Jihar Zamfara, ƙungiyar Ado Allero ta kashe aƙalla fitattun shugabannin ’yan bindiga biyar da mayaƙansu 48.
Rikicin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙauyen Mada da ke Gusau, Yan Waren Daji, da Munhaye a ƙaramar hukumar Tsafe.
Zagazola Makama, ƙwararre a fannin yaki da ’yan tada ƙayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya ruwaito cewa an fara rikicin ne da sanyin safiyar Lahadi. Ƙungiyoyin Dogo Bali da Kachallah Mai Yankuzu ne suka ƙaddamar da shi, lamarin da ya janyo asarar adadin rayuka mai yawa, ciki har da shugaban Dogo Bali wanda ya kitsa harin na farko.
Majiyoyin leƙen asiri sun sanar da Makama cewa mutuwar Dogo Bali ta sa wasu ɓangarorin da ke gaba da juna su dauki fansa. Waɗannan kungiyoyi sun shiga cikin dajin tun daga Hayin Alhaji zuwa Munhaye da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe, inda suke neman ɗaukar fansa kan mutuwar Bali.
Da yake mayar da martani, Kachalla Mai Yankuzu ya kai wa Ado Allero, wanda ya yi gaggawar tara ɗaruruwan mayaka, ya shirya musu arangama. Duk da haka, da isar su sansanin Yan Ware da ke Tsafe, an kama su a wani mummunan harin kwantan bauna da dakarun Allero suka yi.
Rikicin ya dauki tsawon sa’o’i da dama, inda kungiyar Ado Allero ta yi nasarar kashe mayakan da dama da suka hada da fitattun ‘yan bindiga guda huɗu: Dan Makaranta, Malam Gainaga, Malam Tukur, da Malam Jaddi. An kai mayakan da suka jikkata zuwa wani asibiti a kauyen Mada domin yi musu magani.
Yaran Allero ba su tsaya a nan ba; sun kuma kai hari a sansanin Alhaji Dan Nigeria, wani fitaccen shugaban ‘yan fashi da makami a ’Yan Ware. Ɗan Nijeriyar da mayaƙansa sun yi watsi da wurin, inda suka bar bindigu AK47 sama da 150, wadanda kungiyar Allero ta kwace.
No comments