Daga Musa Muhammad Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zu...
Daga Musa Muhammad
Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya ce ya fi 'yan Nijeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Ɗangote ya tabbatar wa da 'yan ƙasa cewa, wasu ne suka ɗauki nauyin yaɗa labarin domin ɓata masa suna a daidai lokacin da 'yan Nijeriya ke cikin halin 'ƙaƙa-na-ƙayi' saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi 'yan ƙasar nan da su yi watsi da labarin, inda Ɗangote ya yi fatan kawo ƙarshen matsalar da ake ciki a Nijeriya.
"Duk abin da ya shafi 'yan Nijeriya ya shafe mu", in ji Sanarwar.
Ɗangote ya para da cewa, ''an kawo maganar faɗuwar darajar Naira da sayen kaya da Dala ne domin cimma wasu buƙatu na kashin kai buƙatun da ba su samu damar biya ba a baya."
Kamfanin na Ɗangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma matatar man fetur. A ɓangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan ɗanyanon girki ne kaɗai.
"Mu ma muna sayen muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yadda kowa ke saye don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al'umma," in ji Ɗangote.
Shugaban kamfanin ya yi mamakin yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin Kamfanonin Ɗangote da ɓangaren gwamnatin tarayya, inda ya ce shi ɗan kasuwa n, ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar Gwamnatin tarayya.
"Kamfanin mu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a kodayaushe, tare da neman sauƙi ga al'umma da fatan alheri."
Saboda haka, sanarwar ta nemi 'yan Nijeriya su guji ɗaudar saƙon da yake ba daga kamfani kai tsaye ba, tare da daina yaɗa raɗe-raɗi da jita-jita.
No comments