Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Taron Kwamitin Tsaron Jihar Zamfara

Daga Musa Muhammad A Talatar nan ne Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jagoranci babban kwamitin tsaron jihar, wanda ya gudana a babban ɗa...

Daga Musa Muhammad

A Talatar nan ne Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya jagoranci babban kwamitin tsaron jihar, wanda ya gudana a babban ɗakin taron da ke fadar gwamnatin jihar a Gusau. 

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa a taron na yau an tattauna batun fito da jami'an tsaron jihar na musamman, waɗanda aka ƙaddamar a kwanakin baya. Haka kuma an ƙaddamar da Hukumar amintattu na kuɗin tsaro. 

Sulaiman Bala ya ce, Gwamna Dauda Lawal ya hori hukumomin tsaro da ke jihar, su haɗa kan su su yi aiki tare don samun nasarar yaƙin da ake yi da rashin tsaro a jihar. 

A lokacin taron, Gwamnan ya jaddada cewa tsaron rayuka da dukiyar jama'a, tare da samar da tsaro, shi ne a sahun gaba na abubuwan da ya sanya a gaban sa. "Wannan taro namu na kwamitin tsaro, ya ta'allaƙa ne wajen bin bahasin yanayin tsaro, tare da lalubo dabarun kare aukuwar hakan. 

“Gwamnati ta kafa jami'an tsaron Zamfara ne bisa shawarwarin ku. A makon da ya gabata an yaye mutum 2,720 a kashin farko, waɗanda kuma yanzu haka an tura su zuwa Ƙananan Hukumomin jihar 14.

“An samar da duk wasu kayan aikin da suka wajaba, wanda ya haɗa ofisoshi a duk Ƙananan Hukumomi 14. Akwai motocin aiki 15 da wasu ƙirar Hilux pick-ups guda biyu ga kowane daga cikin Ƙananan Hukumomi 12, in ban da Gusau da Maru, waɗanda ke da motocin aiki 20 da Hilux hurhuɗu kowannen su. An kuma samar da kayan kare kai, waɗanda suka haɗa da Hulunan Kwano, Takalman Ruwa, Rigunan da harsashi ba ya hudawa, Bindigogin harbi-ruwa da kwanson harsasai. 

“Babban manufar kafa wannan jami'an tsaro, shi ne don su haɗu da 'yan gari, waɗanda suka san lungu sa saƙo na yankunan su, su ƙarfafa wa ƙoƙarin sauran jami'an tsaro. Samun nasarar wannan shiri ya rataya ne ga irin haɗin kan da za a samu daga shugabannin jami'an tsaron da ke jihar, domin waɗ nnan jami'an tsaro na jihar, ba za su yi wani aiki ba, ba tare da goyon bayan sojoji, 'yan sanda da na farin kaya na DSS ba. 

"Ina son sanar da Kwamitin tsaro, cewa a yau an ƙaddamar da hukumar amintattu na kuɗin tsaro. Aikin wannan hukuma, shi ne samo da kuɗaɗen gudanar da harkokin tsaro, da sayo na'urorin da za su taimaka wajen maganin ta'addanci da sauran matsalolin tsaro a jihar."

A ƙarshe Gwamna Lawal ya roƙi shugabannin Hukumomin tsaron, su jajirce, tare da ɗaukar tsauraran matakai, duk da matsaloli da rashin kuɗin da ake fuskanta.

No comments