Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsin Rayuwa: Za Mu Raba Wa Al'umma Kayan Da Mu Ka Ƙwace Daga 'Yan Sumoga -Kwastam

Daga Musa Muhammad A halin da ake ciki dai Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Nijeriya, NCS, ta ce ta kammala shirye-shiryen da suka wajaba don raba...


Daga Musa Muhammad

A halin da ake ciki dai Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Nijeriya, NCS, ta ce ta kammala shirye-shiryen da suka wajaba don raba wasu kayan abincin da kama daga hannun 'yan safara ba bisa ƙa'isa ba a faɗin ƙasar nan, yayin da ake ci gaba da fama da matsalar ƙarancin abinci.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, za a raba kayan abincin ne bayan an tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki matakin ne “domin rage wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci, hukumar kwastam za ta taimaka wajen raba kayan abincin da hukumar ta kama kai tsaye.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Za a sanar da tsarin da za a yi amfani da shi a ofisoshin hukumar da ke faɗin ƙasar, tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci. Mun sha alwashin cewa za a gudanar da wannan aikin domin tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga waɗanda suka fi buƙata.”



No comments