Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ganin an aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar duk da ƙalubalen ...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ganin an aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar duk da ƙalubalen matsin tsadar rayuwa da jama'a da dama ke fuskanta.
Shugaban ya kare sauye-sauyen gwamnatin sa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya, domin abin zai zama alhairi nan gaba kaɗan.
A yayin ganawar sa da wata tawaga daga ƙungiyar kasuwanci ta CCA ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Florizelle Liser, shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa ta ganin ya cimma burinsa na bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya da kuma kawo kwanciyar hankali a ƙasar.
A yayin rantsar da shi ne Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur wanda ya kai ga hauhawar farashin man fetur da sauran wasu sauye-sauye da suka janyo faɗuwar darajar kuɗin naira a ƙasar.
Waɗannan sauye-sauyen dai sun haifar da tsadar rayuwa a Nijeriya irin wadda ba a taɓa ganin irinta ba abin da ya haddasa zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da yajin aiki da dai sauransu.
Amma duk da waɗannan ƙalubale da kuma abubuwan da ke faruwa, Tinubu ya ce ba zai ja da baya ba.
Tinubu ya sha yin kira ga al'ummar ƙasar da su yi haƙuri domin a bar sauye-sauyen nasa su yi tasiri, yana mai cewa za su taimaka wajen jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje, amma matakan nasa na ci wa ’yan Nijeriya tuwo a ƙwarya.
“Na yi farin ciki da cewa ƙungiyar CCA na sha’awar sassa daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya. Muna cikin tsaka mai wuya da fuskantar ƙalubale na sake fasalinmu. Muna da fata, babu shakka, amma ba za mu koma ba,” in ji Tinubu ta bakin mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale.
"Muna fuskantar ƙalubale, kuma mun yi imanin za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen. Ina da hali na 'zan iya cimma wani abu' wanda dole ne a fassara shi zuwa halin wajibi na cimma abin da nake so'. Muna da tawaga mai kyau da kuma tasiri, kuma dole ne mu ci gaba da mai da hankali don cimma burin da aka sa a gaba,” in ji Tinubu.
Tinubu ya kuma yaba da nasarar da aka samu a kwanan baya na samar da wayar ƙarƙashin teku mai tsawon kilomita 45,000 da ta kawo intanet a jihar Akwa Ibom, wanda zai haɗa yankin Kudu-maso-Kudancin Nijeriya da Turai da sauran sassan Afirka.
Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin wannan nasarar, inda ya bayyana cewa idan aka samar da ingantattun manufofi da haɗin gwiwa da azama, Nijeriya za ta iya shawo kan matsalolin da ta daɗe tana fuskanta.
Ya tabbatar da ƙudurinsa na samar da yanayi mai ba da damar kasuwanci don bunƙasa, tare da mai da hankali kan saka hannun jari a muhimman sassa kamar su noma da makamashi da lafiya da fasaha.
No comments