Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Da'awa Islamic Education Trust Fund Sun Horas Da Malamai A Kaduna

...Za Mu Yi Hadin Gwiwa Da Duk Wanda Ke Bukata Daga Imrana Abdullahi Malam Hamza Yusuf, wani mai bincike ne kuma mai aikin bayar da horo a ƙ...


...Za Mu Yi Hadin Gwiwa Da Duk Wanda Ke Bukata

Daga Imrana Abdullahi

Malam Hamza Yusuf, wani mai bincike ne kuma mai aikin bayar da horo a ƙarƙashin Da'awa Islamic Education trust Fund" ya bayyana cewa sun zo Jihar Kaduna ne domin su horas da mutane a kan abin da ake kira shari'a intelligence.

Wato aikin horas wa ne da ya ƙunshi abubuwa guda uku na ilimin addini, wato na farko shi ne Usululfikhu, Kawa'idul fikihiyya sai na uku maƙa'idul shar'iyya.

"Kuma duk lamarin ya samo asali ne bisa ga irin bambanci da kuma zafin ra'ayi na aƙidu da kuma na fahimta da ke cikin addini, saboda haka muna kyautata zaton idan har ilimin ya yaɗu za a samu fahimtar Juna domin za a samu dalili da kuma na kowace mazhaba ce Malamai suka bi a kan hukunce-hukunce na addinin musulunci".

Hamza ya ci gaba da cewa "su ƙungiya ce ta addini sannan kuma ana yin wannan taro ne a ɗakin yin taro na Ƙungiyar Jama'atu Nasarul Islam hedikwata Kaduna. Saboda haka an samo mahalarta wannan taron horaswar ne ta hanyar wasu manyan ƙungiyoyin addini, irin su FOMWAN, JIBWIS, MSS, IMWON, Ƙungiyar Malaman Jihar Kaduna da Nisa'ussunna da dai sauransu, ta hanyar su ne muke yi wa maganar cewa muna buƙatar mu shirya taron horswa sai kowa ya turo mana da wakilai su halarci taron horaswar.

Malam Hamza Yusuf wanda ya kasance mai aikin gudanar da bincike ne ya ƙara da bayanin cewa kamar yadda sunan ƙungiyar ya bayyana da Islamic education trust Burin shi ne a zagaye duniya baki ɗayan ta ba kawai a garin Kaduna ba kawai, kuma a halin yanzu suna yin wani aiki da suke da burin cimma a nan da shekarar dubu biyu da Talatin 2030, akwai yawan adadin mutanen da suke fatan yi wa horaswar nan a kan wannan aikin da muke yi a halin yanzu, kuma za su yi ne a garuruwa da dama na Nijeriya da duniya baki ɗaya da ikon Allah".

A ƙarshe Malamin ya yi kira ga duk wata ƙungiya da ke cikin garin Kaduna ko wajen ta da cewa a shirye suke a yi aikin haɗin gwiwa da duk ƙungiyar da take so a hada Gwiwa game da tabbatar da tafiyar aiki irin wannan da ikon Allah za a bayar da goyon baya dari bisa dari.

No comments