Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bunƙasa Harkar Ilimi: Gwamnan Binuwe Ya Jinjina Wa Farfesa Gwarzo

Daga Musa Muhammad Gwamnan jihar Binuwe, Rabaran Hyacinth Alia ya jinjina wa wanda ya kafa gamayyar Jami’o'n Maryam Abacha American Univ...

Daga Musa Muhammad

Gwamnan jihar Binuwe, Rabaran Hyacinth Alia ya jinjina wa wanda ya kafa gamayyar Jami’o'n Maryam Abacha American University a Nijeriya da Nijer, Franco-British International a Kaduna da Canadian University a Abuja, Farfesa Adamu Gwarzo kan yadda yake nuna kishin ci gaban ilimi a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai wa Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Kano a ranar Lahadi 11 ga watan Faburairun 2024 a daidai lokacin da yake ganawa da ‘yan ƙabilar Tiv mazauna garin Kano a cikin Jami’ar ta Maryam Abacha American University a Kano.

Gwamnan ya fara ne da jinjina wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda ya bayyana a matsayin matashin Farfesa. Inda ya ce Farfesa Gwarzo mutum ne mai son ganin ci gaban ilimi. Kuma mutum ne mai jin ƙan talakawa da waɗanda ba su da shi. 

“Mutum ne mai son sha’anin ilimi sosan gaske. Mutum ne wanda zuciyarsa take jin ƙan talakawa da waɗanda ba su da shi. Mutum ne wanda ya nuna cewa idan Allah ya albarkace ka kai ma ka albarkaci wasu,” in ji Gwamnan.

Ya ci gaba da cewa; “akwai ‘yan asalin jihar Binuwe da dama da suke aiki a wannan Jami’a. Ba kawai a nan ba, har ma da sauran ire-iren waɗannan jami’o’in na shi a Abuja da kuma Kaduna da kuma jamhuriyyar ƙasar Nijer.”

Gwamnan ya ce ya yi matuƙar jin daɗi dangane da shaidar da Farfesa Gwarzo ya bayar dangane da yadda ya yi aiki cikin gaskiya da riƙon amana da ‘yan asalin jihar Binuwe. “shi mutum ne wanda ya kasance abokin mutanen Binuwe. Shi amintaccen aboki ne. Kuma mutum ne wanda ya damu matuka da ci gaban jihar Binuwe."

Farfesa Gwarzo a na shi jawabin, ya yi wa jihar Binuwe fatan alheri. Inda ya ce sun yi sa’ar samun natsattsen mutum a matsayin Gwamna. Inda ya ce “nan ba da jimawa ba talauci zai yi ƙaura daga jihar Binuwe. Za a samu matasan masu kuɗi a Binuwe.

Ya ce yanzu duk wanda ya je Binuwe zai samu jihar ba kamar yadda ya santa ba. “jihar Binuwe ta yanzu jiha ce ta aiki, ba jihar yaɗa ƙiyayya da gaba ba”.

Sannan Farfesa Gwarzo ya ce yana da ɗimbin ma’aikata ‘yan asalin jihar Binuwe wanda ya yi aiki da su, kuma tabbas ya ji daɗin aiki da su. “Na yi aiki da ‘yan asalin jihar Binuwe da dama, na ji daɗin aiki da su, mutane ne masu gaskiya da kamala”, Farfesa Gwarzo ya jaddada.

Farfesan ya ce, ƙofarsa a buɗe take ga mutanen jihar Binuwe, duk abin da suke so su tuntuɓe shi kawai kai tsaye.

A ƙarshe ya zagaya da Gwamnan duk sassa daban-daban na Jami’ar.

No comments