Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Badaƙalar Jabun Sa Hannun Buhari: A Na Tuhumar Mutum Uku Da Hannu A Ciki

A cikin wata mummunar badaƙala ta Miliyoyin Dalar Amurka, wanda ake tuhumar Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele da aikata...

A cikin wata mummunar badaƙala ta Miliyoyin Dalar Amurka, wanda ake tuhumar Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele da aikatawa, inda ya rubuta wata takardar fitar da waɗannan kuɗaɗe da sunan Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya,  Boss Mustapha, tare da yin sanya hannu irin na Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, to yanzu haka wasu mutum uku sun shigo cikin zargin aikata wannan laifi. 

Su waɗannan mutane da ake zargi da laifin rubuta takardar ta bogi, tare da sanya hannun Tsohon shugaba Buhari na jabu, su ne Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Eric Ochem. Kuɗaɗen kuma da aka fitar da waccan takarda ta jabu, sun kai Dalar Amurka Miliyan 6.2, waɗanda aka cire daga Babban Bankin ƙasar. 

Takardun jabun da aka rubuta, su ne:

1. Katin shaidar aiki na wani wai shi Jibril Abubakar, wanda aka nuna yana aiki a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya da ke fadar shugaban ƙasa.

2. Wata takarda da aka ce wai Muhammadu Buhari ya rubuta wa Boss Mustapha, mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Janairu, 2023. 

3. Wata takarda da aka ce Boss Mustapha ya rubuta wa Mr. Godwin Emefiele, mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairu, 2023.

4. Wata takardar cikin gida ta Babban Bankin Nijeriya, wacce aka ce wai Daraktan sashen kula da bankuna ya rubuta wa Gwamnan Babban Bankin.

5. Wata takardar cikin gida ta Babban Bankin Nijeriya, mai kwanan wata 7 ga Faburaru, 2023 wacce aka ce wai Daraktan sashen hulɗa da bankuna ya rubuta ma shugaban reshen bankin na Abuja, da niyyar cewa reshen Abuja na Babban Bankin zai gamsu da cewa takardun nan na gaskiya ne, wanda zai sanya shi ya fitar da waɗannan kuɗaɗe na Dalar Amurka Miliyan Shida da Dubu Ɗari Biyu da Talatin ($6,230,000.00). 

Waɗannan duk suna ƙunshe a wurin kwamitin bincike na musamman da Shugaba Bola Tinubu ya kafa don binciken harkokin Babban Bankin da wasu muhimman cibiyoyin gwamnati. 

In dai za a iya tunawa, shi Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda shi ne aka ce ya rubuta waɗannan takardu, ya bayyana a gaban kwamitin binciken, inda ya bayyana cewa shi sam ba shi da masaniya kan su.

Hukumar EFCC dai tana nan tana binciken waɗannan takardu, tare da sauran badaƙalar da ake tuhumar Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele da muƙarraban sa. 

No comments