'Yan sanda sun harba wa ’yan majalisar dokokin jihar Filato da kotu ta kora su 16 ƙarƙashin jam'iyyar PDP hayaƙi mai sa hawaye. Al...
'Yan sanda sun harba wa ’yan majalisar dokokin jihar Filato da kotu ta kora su 16 ƙarƙashin jam'iyyar PDP hayaƙi mai sa hawaye.
Al'amarin ya faru lokacin da yan majalisar suka isa harabar majalisar tare da magoya bayansu a shirye-shiryen da suke na komawa zama.
’Yan sanda da sauran jami'an tsaro sun mamaye harabar majalisar Fadar gwamnati inda majalisar take tare da hana ’yan majalisar shiga sai dai yan majalisar sun ce ba za su bar wajen ba.
Tsofaffin yan majalisar ƙarƙashin jam'iyyar PDP da kotun ɗaukaka kara ta kora a watan Nuwamba sun yanke shawarar komawa zauren domin ci gaba da gudanar da harkokinsu.
An ruwaito ’yan majalisar da aka kora ƙarƙashin jagorancin Ishaku Maren sun yi dafifi a harabar majalisar tare da magoya bayansu.
Kotu ta kore su ne kan dalilan cewa PDP ba za ta iya gabatar da yan takara ba a zaben 2023 a Filato.
Kotun daga baya ta ayyana mambobin jam'iyyar APC 16 da suka zo na biyu a zaben a matsayin wadanda suka lashe zaɓe.
Duk da cewa tsofaffin ’yan majalisar sun soki lamarin, sun samu kwarin gwiwa bayan da kotun koli ta soke hukuncin kotu da ya kori gwamna Caleb Mutfwang.
A hukuncinta na ranar 12 ga watan Janairu, kotun kolin ta ce karamar kotun ta yi kuskure wajen soke zaɓen gwamnan.
No comments