Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabuwar Jami'ar Fasaha Ta Lafiya Ta Tarayya A Tsafe Za Ta Fara Aiki Nan Ba Da Jimawa Ba -Sanata Bilbis

Daga Hussaini Yero, Gusau An bayyana cewa sabuwar Jami'ar gwamnatin tarayya ta fasahar kiwon lafiya ta Tsafe da ke cikin Jihar Zamfara z...


Daga Hussaini Yero, Gusau

An bayyana cewa sabuwar Jami'ar gwamnatin tarayya ta fasahar kiwon lafiya ta Tsafe da ke cikin Jihar Zamfara za ta fara aiki nan ba da jimawa ba. Sanata Ikira Aliyu Bilbis, Sanata Mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.

Sanata Ikira ya ce ana kan kammala dukkan wasu batutuwa da suka dace da kuma tsare-tsare domin ganin Jami'ar ta fara aiki gadan-gadan.

Ya ce gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ba da wuri na wucin-gadi wanda shi ne wurin dindindin na kwalejin kimiyyar lafiya ta Tsafe mallakar Jihar domin fara karatu a cikinta.

Ya kuma ce nan ba da daÉ—ewa ba Hukumar kula da jami'o'in za su turo Mataimakin Shugaban Jami'ar da Manyan Ma'aikata don fara aiki a sabuwar Jami'ar gadn-gadan.

Daga nan Sanata Ikira ya yaba wa shugaban Æ™asa Bola Ahmad Tinubu bisa goyon bayan kafa jami’ar domin samar da Æ™wararrun ma’aikata a fannin kiwon lafiya a faÉ—in Æ™asar nan.

Sanata Bilbis ya kuma yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa samar da matsugunin wucin gada da Jami'ar za ta fara.
 

No comments