Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa manyan nasarorin da ya samu, inda ya jaddada kyakkyawan t...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa manyan nasarorin da ya samu, inda ya jaddada kyakkyawan tasirin shugabancinsa a Jihar Zamfara.
A ranar Talata ne tsohon shugaban ƙasar ya ƙaddamar da asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da wasu manyan tituna guda biyu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa a karon farko jihar ta samu na’urar É—aukar hoton jikin É—an adam mai gani jar hanyi, ta 'CT Scan,' da wata na’urar ita mai É—aukan hoton dukkan sannan mutum, ta 'MRI Machine' a asibitin Æ™wararru na Yariman Bakura da aka gyara.
A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya.
Tsohon shugaban Æ™asar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba, mai ci gaba kuma sabuwar Zamfara a Æ™arÆ™ashin jagorancin ka.
“Ga mu nan. Abubuwa biyu sun ba ni mamaki: Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa kun samar da na'urorin CT scan da MRI Machine, na san wasu asibitocin koyarwa ba su da CT scan da MRI, wasu kuma suna da shi amma ba sa aiki. Ku ga na ku, yana aiki ga al'umma.
"Na yi matuƙar farin cikin kasancewa a nan, don ƙaddamar da wannan asibitin da aka gyara da kuma saka kayan aiki na zamani don jin daɗin duk wanda zai zo nan."
Da yake ƙaddamar da titin Zannah zuwa Abarma, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya bayyana cewa, Gwamna Lawal na mayar da Zamfara jiha ta zamani.
"A bisa abubuwan da na gani da idanu na da kuma wanda na ji, mu abokan haɗin gwiwa ne a ci gaba. Ina roƙon ka da ka ci gaba da inganta jihar Zamfara a tsawon shekaru takwas da gwamnatin ka za ta yi."
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya gode wa tsohon shugaban ƙasa Obasanjo bisa amsa gayyatar da aka yi masa na ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar.
“Ranka ya daÉ—e, a madadin É—aukacin al’ummar jihar Zamfara, muna godiya da karrama mu ga amsa gayyatar da muka yi maka, da kuma maraba da zuwa gidanka na biyu, Jihar Zamfara, Jihar da ka ke kyauna a zuciyarka, domin sana’armu ta farko a nan ita ce noma, kuma wani abu ne da ka ke sha’awa.
“Asibitin Æ™wararru na Ahmad Sani Yariman Bakura ya bi tsarin faÉ—aÉ—awa da ingantawa, an kuma gina sabbin gine-gine, a yanzu haka likitocin suna da sabbin gidajen zama da aka kammala, waÉ—anda suka haÉ—a da rukunin gida mai É—akuna biyu da mai uku, da kuma wurin zama da ya dace da Babban Daraktan Lafiya.
“An kuma samar da filin da mara lafiya zai shaÆ™atawa cikin natsuwa tare da Æ™awata yanayin asibitin. Mun kuma inganta hanyoyin cikin asibitin don sauÆ™aÆ™a zirga-zirga da Æ™ayatar da harabar asibitin.
“Sabbin cibiyoyin da aka gina su ne Sashin Kula da Mata (O&G), sabon rukunin Radiology, sashin É—akin gwaje-gwaje, da filin shaÆ™atawa na marasa lafiya.
“GinshiÆ™i shi ne gyara muhimman sassa guda 14, waÉ—anda dukkansu an sake farfaÉ—o da su tare da inganta su zuwa matsayin zamani.
"Mun saka duk waɗannan kayayyaki na zamani a wuraren da suka dace kuma masu muhimmanci. Waɗannan sun haɗa da saka na'urori na zamani a bangaren don radiology, wankin ƙoda, tiyata, ophthalmology, ENT, physiotherapy, endoscopy, echocardiography, haƙori, da kuma kula da lafiya gaba ɗaya.
"An kuma ba wa asibitin sabbin gadaje na majiyyata, na'urorin lantarki, kayan ɗaki, da kayayyakin tattara shara don tabbatar da tsaftar muhalli da bin ƙa'idojin tsabta na duniya."
Gwamnan ya jaddada cewa asibitin yana da ingantattun kayan aiki don aiki a matsayin cibiyar tuntuÉ“ar likitoci, ingantaccen wurin horar da ma’aikatan kiwon lafiya kuma cibiyar bincike da Æ™ididdiga ta likitanci.
Sauran ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da titin Zannah zuwa Abarma da titin Tsalha Bungudu zuwa Kwanar Birnin Ruwa, duk a Gusau babban birnin jihar.
No comments