Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dawowar Mulkin Dimokraɗiyya A Ƙasar Nan Na Tattare Da Nasarori -Haruna Wakili

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana cewa dawowar tsarin mulkin Dimokraɗiyya a ƙasar nan a shekaru 26 akwai ɗimbin nasarori da aka samu, d...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana cewa dawowar tsarin mulkin Dimokraɗiyya a ƙasar nan a shekaru 26 akwai ɗimbin nasarori da aka samu, da kuma  ƙalubale mai tarin yawa da ya jefa al'umma a cikin kunci.

Ɗaya daga cikin matasan ‘yan siyasa a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Hon. Haruna Kabiru Wakili ne bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Wakilin mu a Kano.

Ya ce idan aka yi duba ta fuskar siyasa an yi shugabanni guda biyar daga 1999-2025. Tun da aka karɓi mulki daga sojoji aka zaɓi Obasanjo har zuwa marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua har aka kai ga Jonathan da Buhari ya karɓi mulki a wajensa, sannan har aka zo ga shugaba na yanzu Bola Ahmad Tinubu ba a sami yankewar tsarin mulkin farar hula ba.

Ya ƙara da cewa babu wani shugaba da ya zo ya miƙa mulki daga soja ya bai wa farar hula tun daga Obasanjo a mulkinsa na soja da ya bai wa Alhaji Shehu Shagari tun daga nan sai dai a yi ta juyin mulki, har sai lokacin da aka yi gwamnatin Abdussalam Abubakar da ta bai wa Obasanjota a matsayin zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa, tun 1999 ake ta tafiya ba tare da yankewa ba.

Ya yi nuni da cewa wannan ta fuskar cigaban siyasa abu ne mai kyau, sai kuma nasara da aka samu a ƙasar nan ta haɓakar tattalin arziƙi, wanda kafin 1999 ba za a iya sanya ƙarfin arziƙin ƙasar nan a matsayi mai yawa ba, amma yanzu ya nunka, ana samun kuɗaɗen shiga da bunƙasar tattalin arziƙi. In aka dubi wannan za a iya cewa demakraɗiyya ta yi amfani a shekaru 26 da dawowa.

Hon. Haruna Kabiru Wakili ya ce sai dai kuma dimakraɗiyyar ta kawo matsaloli, domin har yanzu ƙasar nan a harkar dimakraɗiyya a matsayin koyo ake har yanzu. “Akwai ƙarancin wayewa, ana amfani da ‘yan daba wajen yin zaɓe, ba a barin talakawa su zaɓi abin da suke so, kuma ba a daina sauya sakamakon zaɓe ba a matattar hada-hadar zaɓe ba.

Ya ce har yanzu ba mu sami cikakkiyar wayewa ba a zaɓe ya kamata a ce zaɓen ma ta na’ura mai ƙwaƙwalwa ake ya zama a ko’ina kake za ka iya zaɓar ɗan takara da jam”iyyar da kake so ko a ina kake a duniya ba ma a ƙasar nan ba.

Wannan zai tabbatar da gaskiya, yanzu mutanen ƙasar nan sun kai sama da miliyan 200, amma abin takaici ko miliyan 20 ba sa yin zaɓe, domin ko shugaban ƙasa da yake kai yanzu da ƙuri’a da ba ta wuce miliyan takwas ce ta kawo shi mulki ba, duk raguwar ‘yan takarar inka haɗe da ƙuri’unsu ba su wuce miliyan 22 ba. Wannan babban ci baya ne.

Hon. Wakili ya ce sai kuma ƙalubale da aka samu na tattalin arziƙi, musamman yadda jama’a suke shiga halin ƙunci da har mutane ke ganin an jefa su a matsin tattalin arziƙi don sai a ce an janye tallafi an kuma karɓi ba shi a ƙasashe da hukumomi na duniya wanda daga 1999 zuwa yanzu ba a taɓa samun mutane sun shiga cikin cikin mawuyacin halin matsin rayuwa irin na wannan lokaci ba hakan tasa mutane sun soma baya-baya da tsarin dimakraɗiyya.

Ya ce daga lokacin da tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya soma cire tallafi zuwa lokacin da Tinubu ya karɓi mulki za a ga cewa akwai koma-baya sosai ta fuskar tattalin arziƙi.

Ya ce, domin a baya Nijeriya tana ɗaukar kambun zama ta kan gaɓa a ƙarfin tattalin arziƙi a tsakanin ƙasashen Afirka, amma yanzu abin takaici saboda manufofi na cin ba shi da ake na bankunan duniya da hukumomin lamuni sai da masu arziƙin mu suka yi baya a jerin masu arziƙi na duniya saboda tattalin arziƙi ya koma baya saboda karya darajar Naira masu kuɗi in suna da biliyan 12 ya koma 10.

Wannan ya jawo koma-baya mutane yanzu da yawa ba sa iya sayen kayan more rayuwa wanda durƙushewar tattalin arziƙi yana shafar al’ummar Nijeriya yana shafar walwala da jin daɗin ‘yan ƙasa wanda yake ɗaukar albashi baya iya kai shi wata guda wannan koma baya ne a dimakraɗiyya.

Ya ƙara da nuni da cewa a da kuma za ka ga malamai da sarakuna sune alƙiblar mutane sune suke cewa a yi kaza ko kar a yi kaza, amma yanzu siyasa ta zo ta raba waɗannan shugabanni ba a ba su darajarsu irin ta baya. Wannan ya jawo ‘yan siyasa suna iya juya Malami ya zama nasu, wannan Malami a ce ɗan jam’iyya kaza ne wasu kuma ‘yan kaza ne.

Haka su kuma kan al’umma ya rabu idan Malami yana wata jam’iyyar sai yaƙi zuwa wancan masallacin saboda ba jam’iyyarsu ɗaya ba. Su ma sarakuna an raba su kimarsu na zubewa a tsakanin mutane.

Ya ce idan aka ɗauki yanayin shekara biyu na mulkin Tinubu za a iya cewa an kawo wani gwani ne na siyasa da ya san siyasa tun daga tushe, wanda a yanzu dai a ƙasar nan ba wanda yake da tsari na siyasa kamar yadda ya haɗa nasa.

Shi ya sa yanzu duk da kokawa da ake da mulkinsa za ka ga ya zama gwarzo yadda yake ta ƙoƙarin murƙushe ‘yan adawa in aka duba matakai da yake ɗauka na hana ‘yan siyasa da jam’iyyun adawa su haɗa kansu irin su.

PDP,, APGA, LP da NNPP an hana su zaman lafiya, wanda shi sama da shekaru 24 yana cin gajiyar adawa in aka ɗauke shekara takwas ɗin Buhari.

Wannan abin ya sa yadda adawa take da tasiri wajen kawar da gwamnati, idan har zai yi shekara 16 yana adawa da har akwai lokacin da gwamnatin Olusegun Obasanjo ta hana shi kuɗin ƙananan hukumomi da wasu haƙƙoƙi na jihar Legas lokacin yana Gwamnan jihar saboda adawa da yake a haka har ya zama jihohin Kudu maso Yamma na hannunsa matsayinsa na jigo a siyasar yankin da wannan dama ne ya yi amfani har ya shiga haɗaka aka kafa APC aka sami nasara. Wannan ya ba shi dama ya san yadda siyasar Nijeriya take da kuma abin da ‘yan siyasar ƙasar nan suke so ya yi musu.

Ya ce shi ya sa duk mutumin da ya san zai ba shi matsala ya sha alwashin da ƙoƙarin ganin kafin shekara ta 2027 ta ƙaraso, sai ya tabbatar yana ɓangarensa wannan kuma tsarin yana yi cikin nasara a siyasance yana yin abin da yake so siyasarsa ta cigaba, amma abin tambaya a nan shi ne a siyasar Nijeriya cigaba aka samu ko koma baya?

Magana ta gaskiya idan aka ce ‘yan adawa ba su da ƙarfi hakan zai iya sawa a sami matsala da zai hana mutane su zama ba su da fata, dama idan akwai adawa ne mai ƙarfi mutane suke iya jin suna da dama wanda yake kai idan baya abin da ya kamata a lokacin zaɓe za su sauya shi da wata jam’iyya, amma yanzu jiga-jigai da za su kare maka ƙuri’a ma in ka ci zaɓe sun tafi sun bar jam’iyyar adawa.

Don haka ko an zo zaɓen sai a iya zuwa a juya shi a wani waje wannan abu ba mai kyau ba ne hakan na iya sawa su wanda ke kan mulki su ga cewa ko ka zaɓe su ko ba ka zaɓe su ba za su iya cin zaɓen, domin suna da ƙarfi a sama. Wannan zai sa su ƙi kulawa da yin abin da ya kamata, amma idan kullum suna tunawa za su dawo wajen masu zaɓe, kuma sun san ‘yan adawa suna da ƙarfi wannan zai ƙara taimaka musu wajen ƙara damara da himma. kullum su yi abin da ya kamata domin mutane su amfani dimakraɗiyya.
 

No comments