Daga Musa Muhammad Ministan Babban birnin tarayya, Abuja, Ezenwo Nyesom Wike ya bayyana cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar amin...
Daga Musa Muhammad
Ministan Babban birnin tarayya, Abuja, Ezenwo Nyesom Wike ya bayyana cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar amincewar gaggawa don sayo na'urar da za ta taimaka wajen gano maɓoyar 'yan ta'adda, na'urar kuma irin ta zamani ce.
Ministan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar jiya Litini a Abuja, inda ya yi ƙarin haske da cewa, masu kai wa 'yan ta'addan bayanan sirri (informants), waɗanda aka kama, suna nan suna bayar da haɗin kai wajen tatsar muhimman bayanai game da ta'addancin.
Haka kuma Wike ya yi ƙorafin cewa jami'an tsaron da ke Abuja ba su da isassun kayan aiki. Ya ce, "Ba a samar da isassun kayan aiki ba. Babu motoci ga jami'an tsaro. Abin mamaki, babu kayan aikin da za a iya gano maɓoyar miyagu, sai dai kawai in wani abu ya faru, sai su garzaya ofishin Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ko kuma su je Hedikwatar 'yan sanda. Sam ba haka ya kamata abin ya kasance ba.
“Lokacin ina Gwamnan jihar Rivers, jami'an tsaro na DSS sun shaida mani suna buƙatar wasu kayan aiki, na ba su izini, mu kaɗai ne muka mallaki irin wannan na'urar a lokacin. Ina tabbatar maka, hatta Hedikwatar su, da ita su kan yi amfani.
"Irin waɗannan kayan aikin, na'ura ce ta musamman, kuma irin ta muke nema a nan. Na san tana da tsadan gaske, amma lallai muna buƙatar ta, domin za ta rage mana ayyukan ta'addanci.
“Haka kuma, kafin mu zo shugabancin Abuja, 'yan sanda sun nemi a sayo masu babura domin shiga inda mota ba ta iya zuwa. Amma abin takaici ba a samar masu ba, to mu yanzu za mu samar da su.
“A harkar tsaro, bayan kayan aiki, su ma jami'an tsaron suna buƙatar kulawa. Ba na son yin magana game matakan da za mu ɗauka, domin muna magana ne bisa tsaro yanzu."
No comments