Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikakken Bayanin Dokar Harajin Da Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu A Kai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Sabbin Dokokin Gyaran Haraji, wanda ya kawo sauyi mai girma a tsarin harajin Nijeriya. A mats...


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Sabbin Dokokin Gyaran Haraji, wanda ya kawo sauyi mai girma a tsarin harajin Nijeriya. A matsayinka na É—an Nijeriya, wannan doka ta shafa ka kai tsaye.

Ga ƙarin bayani don a fahimta yadda wannan doka ke shafar ka:

1. Canjin Sunan FIRS: An sauya sunan Federal Inland Revenue Service (FIRS) zuwa Nigeria Revenue Service (NRS).

2. ÆŠaure Cikin ÆŠaya na Tarin KuÉ—in Haraji: NRS zata É—auki nauyin tarin haraji da kudaden shiga da wasu hukumomi ke tarawa a baya kamar su Nigeria Customs Service, NUPRC, NPA, da NIMASA.

3. SauÆ™in Haraji ga Ma’aikata Masu Ƙananan KuÉ—i: Ma’aikatan da ke samun Æ™asa da Naira 800,000 a shekara ba za su biya haraji ba.

4. Haraji ga Masu Babban KuÉ—i: Ana sa harajin kashi 25% na kuÉ—in shiga ga mutane da ke samun sama da Naira miliyan 50 a shekara.

5. ’Yancin Haraji ga ’Yan Kasuwa Masu Ƙanana: Masu Æ™ananan sana’o’i ba za su biya harajin kuÉ—in shiga ba gaba É—aya.

6. Rage Harajin Kamfanoni: Daga shekarar 2026, za a rage harajin kuÉ—in shiga na kamfanoni matsakaita da manya daga kashi 30% zuwa 25%.

7. Rage VAT akan Abubuwan Bukata: Ba za a sa VAT (harajin kaya da sabis) akan muhimman kayayyaki ba irin su abinci, ayyukan lafiya, magunguna, kudin makaranta, da wutar lantarki.

8. Babu Ƙarin Haraji: VAT ya ci gaba da kasancewa a kashi 7.5%, kuma harajin kamfanoni yana nan a kashi 30%—ba a Æ™ara komai ba.

9. Sabon Kuɗin Ci Gaban Ƙasa: Za a fara cajin Development Levy daga kashi 2% zuwa 4% don tallafa wa cibiyoyin ƙasa masu muhimmanci kamar su NELFUND, TETFund, NITDA, da NASENI.

Ƙarin Bayani Daga Shu'aib Kabir
 

No comments