Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take. ...
Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.
Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya da ya ajiye muƙaminsa.
Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.
Lokacin da ya kwashe a matsayin shugaban jam’iyyar na cike da cece-kuce da suka.
Ko da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.
Haka kuma, an danganta murabus ɗinsa da zarge-zargen almundahana da karkatar da kuɗaɗe.
Wasu ’ya’yan jam’iyyar sun koka cewa ofishinsa na tilasta musu biyan kuɗi da yawa, musamman masu neman tikitin takara a Abuja.
Murabus ɗin Ganduje babban sauyi ne ga shugabancin jam’iyyar APC.
Yanzu haka, mutane da dama suna jiran su ji yadda jam’iyyar za ta shawo kan wannan lamari.
Har yanzu jam’iyyar APC ba ta fitar da wata sanarwa kan murabus ɗinsa ba.
No comments