Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Al'ummar Mu Suna Zaman Lafiya Da Kyakkyawar Dangantaka Da Jama'ar Kano -Shugaban Al'umma

An bayyana haɗa kan al'umomin da ke Arewa maso Gabashin ƙasar nan a Kano, waɗada suka ƙunshi na Barno,Yobe, Adamawa, Bauchi, Gwanbe da T...

An bayyana haɗa kan al'umomin da ke Arewa maso Gabashin ƙasar nan a Kano, waɗada suka ƙunshi na Barno,Yobe, Adamawa, Bauchi, Gwanbe da Taraba ta sa aka samar da inuwar al'umomin mazauna jihar Kano, inda kuma su ke zaune lafiya da sauran Al'ummun da ke Kano.

Mai Kanuribe I, Shugaban al'ummar yankin mazauna jihar Kano, wanda ya ke kuma Wakilin Shehun Barno Alhaji Mustapha Lawan ne ya bayyana hakan.

Ya ce al'ummomin su suna da yawa a jihar Kano tun iyaye da kakanni suke, sun haifi 'ya'ya da jikoki da suka zama bangare na  al'ummar jihar suke bayar da gudumuwa ga ci gaba a fannoni da dama.

Ya ce, a da  ba su da wakilin da yake wakiltar su don haɗa kai da kare muradun su, don haka aka ba shi damar ya yi wannan wakilci da yake akai yanzu sama da shakaru uku ke nan, kuma suna  da wakilai a dukkan Ƙananan Hukumomi 44 a jihar kano .

Mai Kanuribe ya ci gaba da cewa, ba za su iya ƙiyasta yawan al'ummar su ba, domin a wasu Ƙananan Hukumomi, irin su Bichi, Dawakin Tofa da sauran wasu da yawa suna da al'ummar Kanuri da wasu har sun yi sarauta a Gaya.

Alhaji Mustapha ya ce sun godewa Allah al'ummar su da ke Kano na bada gudumuwa wajen zaman lafiya kulum, sannan  ya yi  kira gare su su ci gaba da bayar da haɗin kai wajen inganta zaman lafiya.

Ya ce a taruka da sukan yi da al'ummar suna dada   jan hankulansu su guji shiga duk wani abu na rashin kyautawa da zai haddasa fitina, iyaye su bai wa 'ya'yan su kyakkyawan tarbiyya. Su kuma Matasa su zama masu tarbiyya da neman ilimi da yin sana'oi na dogaro da kai da doka ta amince da shi akan hakan, kuma suna ba su goyon baya da ɗaukar nasiha da ake musu.

Wakilin na Shehun Barno ya ce suna da kyakkyawar dangantaka da masarautar Kano da sauran masarautu kamar yadda tun asali a tarihi  akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin   masarautar Barno da al'ummar Arewa ta Gabas da masarautar Kano.

A ƙarshe Alhaji Mustapha Lawan ya yaba da irin ɗimbin ƙoƙari da gwamnatin jihar Kano a  ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam suke yi wajen gudanar da muhimman ayyuka na bunƙasa ci gaban al'umma a fannoni daban-daban da kuma kyautata harkar ilimi da inganta tsaro.
 

No comments