Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za A Samu Tashoshi 20 A Hanyar Jirgin Ƙasa Na Kano Zuwa Maraɗi, Aikin Ya Kankanma

Aikin gina hanyar dogo daga Kano zuwa Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar yana ci gaba gadan-gadan. Ana sa ran nan gaba kaɗan jirgi zai fara bi ta ka...


Aikin gina hanyar dogo daga Kano zuwa Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar yana ci gaba gadan-gadan. Ana sa ran nan gaba kaɗan jirgi zai fara bi ta kan hanyar.

Shi dai wannan aiki, gwamnatin Buhari ce ta fara shi, sannan gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aiwatar da shi.

Idan an kammala aikin, za a samu tashoshi 20, gadoji 52, da wurare sama da 80 inda hanyoyin mota suka gitta a kan hanyar. Haka kuma, kaya mai nauyin kimanin tan 3,000 da kuma fasinjoji 9,374 za su bi kan hanyar a kullum, sannan hanyar za ta haɗu da hanyar dogo ta Kano zuwa Legas.

Kammala hanyar a bana zai kasance ɗaya daga cikin muhimman nasarorin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu a zamanin ta.
 

No comments