A kwanakin baya ne Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gabatar da wata tattaunawa ta musamman don cikar sa shekara biyu a karagar mulki, w...
A kwanakin baya ne Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gabatar da wata tattaunawa ta musamman don cikar sa shekara biyu a karagar mulki, wacce ta gudana a ofishin sa da ke Gusau.
A cikin wannan tataunawa, wacce MAHDI MUSA MUHAMMAD ya fassara, ya rubuto, Gwamna Lawal ya yi bayanai cikakku game da matakan tsaro da gwamnatin sa ta ɗauka, da yadda yake ƙoƙarin sauya fasalin jihar, da manufar sa ga jihar a shekaru biyu masu zuwa, takararsa karo na biyu da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar sa ta PDP, da dai sauran bayanai.
A biyo mu. Ga dai yadda hirar ta kasance:
A cikin ’yan kwanakin nan ka aiwatar da ayyuka da dama. Za ka iya mana ƙarin bayani game da wannan?
Abin farin cikin, kasancewar ku a nan a yau, kuma na yi farin ciki da yadda ku ke iya ganin ayyukan da aka aiwatar da kan ku. Kamar yadda ku ka ambata, an ƙaddamar da ayyuka da dama. A ranar Litinin, Minista ya ƙaddamar da ginin ma'aikatar harkokin mata - da aka sake ginawa kuma aka inganta - tare da gyara ajujuwa da ɗakunan kwanan ɗalibai a Kwalejin Fasaha da Kimiyya. A jiya ne tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya ƙaddamar da Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura wanda muka sake ginawa gaba ɗaya. Wannan dai shi ne karon farko da Zamfara ke samun irin wannan sauyi, musamman a fannin lafiya. A watan Disamba 2023, bayan na ziyarci asibitoci daban-daban - musamman a Gusau, na yi mamakin ganin irin yanayin da suke ciki. Hakan ya haifar da ayyana dokar ta-baci a fannin lafiya a ranar 31 ga Disamba, 2023.
Na kafa tawagar ƙwararru don tantance wuraren kiwon lafiya a duk ƙananan hukumomin jihar. Binciken nasu ya buƙaci a ɗauki matakin gaggawa. Mun fara ne a garin Nasarawa ta hanyar mayar da cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko zuwa cikakken asibiti - na farko a Zamfara. Mun sake maimaita wannan tsari a Maradun, Maru, Ƙauran Namoda, da Buzu, inda aka haife ni. Mun tabbatar da cewa kowane ɗayan waɗannan asibitoci an sanye shi da fasahar zamani kuma ana samun tsayayyen wutar lantarki don tabbatar da aiki a kowane lokaci.
Babban muhimmin ci gaba a yanzu shi ne asibitin da Obasanjo ya ƙaddamar. Mun shigar da sabbin kayan aiki, gami da sabon na'urar CT ta ɗaukar hoton cikin jikin ɗan adam da injunan MRI - mafi kyau a cikin ƙasar. Obasanjo ya yi mamaki. Yanzu muna da cikakken sashin 'Radiology' wanda zai iya ba da sakamako cikin mintuna.
Shin akwai wasu ƙarin ayyuka da ke tafe?
Lallai akwai. A cikin watanni biyu masu zuwa, za mu ƙaddamar da sabbin manyan asibitoci a Sifawa da Fifi. Waɗannan sabbin gine-gine ne gaba ɗaya. Na ziyarci ɗaya daga cikin tsofaffin asibitocin kuma na sha mamaki. Ba mutumin da zai yarda ko da dabba a yi masa magani a wurin. A lokacin ne na san da gaske aikin ceto ne zan yi. Amma ba kawai game da gini ba. Muna kuma buƙatar ƙwararrun ma'aikata. Don jawo hankalin su, mun gyara albashin likitoci don ya zama daidai da matakin tarayya. Gine-ginen da ba su ƙwararru ba su da amfani. Har ila yau, muna saka hannun jari don haɓaka komai. Mun inganta makarantun koyon aikin jinya guda biyu - ɗaya a Tsafe ɗaya kuma a Birnin Magaji - an ƙara sabbin ajujuwa, ɗakunan kwanan ɗalibai, manyan ɗakuna ɗaukar karatu, da kayan koyarwa na zamani. Muna son yaye ƙwararru a fannoni kamar haƙora, kunne da maƙogwaro, da dai sauran su.
Burina shi ne in tabbatar da cewa babu wani ɗan jihar Zamfara da ke buƙatar barin jihar domin neman lafiya. Da yunƙurinmu, hakan na zama gaskiya.
Idan muka tabo bangaren tsaro. Lokacin da na shirya wannan ziyara, sai na tambayi manhajar ChatGPT ko babu damuwa zan iya tafiya zuwa Gusau, Jihar Zamfara? Amsar ita ce tafiyar tana da haɗari, kuma a bisa shawara kar na yi ta sai ta zama dole. Mene ne ra'ayinka?
Wannan tsohon labari ne. Labarin tsaro ya canja. Tsaro ya inganta sosai. Kai ɗan jarida ne - duba sababbin bayanan ga gani. Kwatanta abubuwan da suka faru na garkuwa da mutane da kashe-kashe yanzu da shekaru biyu da suka gabata. Akwai bambanci ba ɗan kaɗan ba.
Mun yi ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro, ’yan fashi, garkuwa da mutane, da satar shanu. A da ambato Zamfara kawai ke tsorata mutane. Amma da ka zo ta hanya daga Zariya, me ka gani? Manoma sun koma gonakinsu, tituna sun cika kuma mutane na tafiya cikin walwala.
Lokacin da na hau mulki, na san akwai buƙatar fitar da sabon tsari. Shi ya sa muka ƙirƙiro Rundunar Kare Al'umma (CPG) wato ‘Askarawan Zamfara’. Sama da maza 3,000 ne aka ɗauka aiki, waɗanda sojoji da DSS suka horar. Kafin ɗaukar ma'aikata, mun zartar da doka ta Majalisar Jiha don sanya rundunar ta zama doka. Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kuma ba da bayanan kowane mutum don tabbatar da gaskiya. Yanzu haka dai waɗannan Askarawa suna tallafa wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
Duba da tsofaffin gwamnoni kamar Matawalle da Yari a Jihar Zamfara, kana da garantin za su ba ka damar komawa wa'adi na biyu?
Bari in tambaye ka, a 2023, duk manyan jiga-jigan APC - Matawalle, Yari, mataimakan su - har yanzu dukkan su suna APC? Ni kaɗai ne a PDP, amma ga ni. Nufin Allah kenan. Na gaskanta iko daga wurin Allah yake. Dangane da ko ni ne gwamnan Matawalle da Yari - eh, ni ne. Ni ne gwamnan kowane ɗan jihar Zamfara.
Manufofinmu na kowa ne, ba ’yan PDP kaɗai ba.
Shin ka damu da batun Arewa maso Yamma tana neman zama yankin jam'iyya ɗaya?
A'a. Ban damu ba. Ni ma ban fidda rai ba. Na gansu da inda nake. Ni ɗan PDP ne kuma zan ci gaba da zama a PDP. Idan Allah Ya ce zan sake yin nasara a 2027, babu mai iya hanawa.
Amma PDP na fama da rikicin cikin gida, mene ne mafita?
Kowace jam'iyya tana da matsalolin ta. Za mu warware ta mu. Muna da taron Kwamitin Gudanarwa ta NEC da aka shirya yi karo na 30. Haka ne, akwai matsaloli, amma za a gyara su. Ina cikin kwamitin sulhu da Sanata Bukola Saraki ke jagoranta. Muna aiki ba dare ba rana don gano bakin zaren. Babu wani abu da ba za a iya magancewa ba.
Wasu dai na ganin takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a jam'iyyar ita ce babbar matsalar PDP. Ka yarda da hakan?
A gaskiya, ba na tunanin komai game da Atiku ne. Matsalolin sun wuce shi. Al’amari ne na cikin gida a cikin PDP, kuma muna ƙoƙarin warware shi. Ina tsammanin matsala ce ta kowa.
Shin kana ganin Nijeriya za ta taba yin zabe cikin gaskiya da adalci?
Eh, ina yi. Na fuskanci hakan a Zamfara. Duk da irin taron dangi da aka min, an zabe ni. Ya kasance cikin da gaskiya da adalci. Kuma na yi imani zai iya sake faruwa. Lokaci ne kawai.
A baya ka ambaci Rundunar Kare Al'umma (CPG). Ko za ka iya bayyana yadda aka ɗauke su aiki da kuma ayyukan su?
Bayan an yi nazari a hankali, an gabatar da jerin sunaye wanda muka yi amfani da su a kan haka. Mun ba da horon da ya dace kan yadda ake tafiyar da al’amuran tsaro tare da zayyana nauyin da ke kansu. Ba a nufin su cutar da kowa - an kafa su ne don kare al'umma ne.
Mun ɗauke su aiki daga dukkan ƙananan hukumomi saboda mun yi imani da neman mafita na cikin gida. Komai a Zamfara na gida ne. Babu wani daga waje. Waɗannan mutanenmu ne, suna da sani kan yankunan Zamfara. Sauran jami’an tsaro su ma suna aiki da su saboda sun san ko su wane ne waɗannan mutanen, waɗanda ke taimaka wa ayyuka.
Suna aiki a matsayin layin farko na tsaro. Mun saka hannun jari sosai - dabaru, kayan aiki, makamai, motoci - da dai sauran su. Kuma ina farin ciki da sakamakon da hakan ya haifar. Wannan shiri ya maido da fata ga jama'a. A yanzu gwamnati ta san akwai tsaro. Ƙoƙari ne mai gudana, kuma mun himmatu don ci gaba da tabbatar da shi.
Me ya sa abubuwa suka yi muni kafin ka hau mulki? Har ila yau, wane irin haɗin kai ka ke samu daga hukumomin tsaro na ƙasa, kuma ta yaya kasancewar magabacinka Ƙaramin Ministan Tsaro a halin yanzu yake shafar aikinka?
Da farko, bari in bayyana wannan a sarari: akwai haɗin kai mai ƙarfi tsakanin Askarawan Zamfara da hukumomin tsaro na ƙasa — sojoji, ’yan sanda da sibil defens.
Lokacin da na hau mulki, ni da kaina na ziyarci Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Babban Hafsan Sojin Sama, Babban Hafsan Sojin Ruwa, Babban Hafsan Tsaro, da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro. Ina so in fahimci abin da gwamnatin tarayya ke yi da kuma gano wuraren da za a yi haɗin gwiwa. Abin da na sa a gaba shi ne tabbatar da tsaro a Zamfara, kuma na samu haɗin kai, duk da cewa dole ne a ci gaba da gudanar da aiki domin shugabanci a waɗannan hukumomi na canjawa akai-akai.
A matsayina na gwamna, ba wai goyon baya da baki kawai nake yi ba; Ina kuma taimakawa da kuɗi. Muna ba da man fetur, kayan aiki, da sauran albarkatu ga hukumomin tsaro don taimakawa wajen tabbatar tsaro a Zamfara.
Game da Ministan Tsaro, eh, na yi ganawa da shi. Na bayyana halin da muke ciki, har ma ya ziyarci Zamfara. Mun zagaya yankunan da abin ya shafa tare, kuma na yi imanin ya fahimci muhimmancin al'amuran. Haɗin gwiwarsa yana taimakawa, amma dole ne mu ci gaba da nuna ƙwazo. Waɗannan ƙalubalen tsaro sun dawwama tsawon shekaru 13. Ba mu ƙirƙire su ba, amma mun gaji su kuma dole ne mu magance su.
Me ka ke gani a matsayin tushen wannan matsala?
Abin takaici ne, amma dole ne faɗi gaskiya. A Zamfara, kashi 99.9 na mutanenmu Hausa-Fulani ne kuma galibinsu Musulmi ne. To me ya sa hakan ke faruwa? Daga binciken da na yi, an fara ne da wata ‘yar rashin fahimta tsakanin Bahaushe da Bafulatani. Ba a warware shi yadda ya kamata ba, kuma wani bangare yana jin an hana shi adalci. Cikin takaici sun kai hari wani ƙauye inda suka kashe mutane biyu suna tsammanin gwamnati za ta shiga tsakani. Amma babu abin da ya faru. Wannan rashin katabus ya ba su ƙwarin gwiwa, kuma rikicin ya ƙaru.
Da zarar aka yi sakaci da rikici, sai ya zama ala-ƙaƙai. Kuma abin takaici, yawancin mutanen da abin ya shafa talakawa ne, mutanen da ba su da komai. A yankin Neja-Delta, tsageru suna yin artabu a kan man fetur. A wani wurin kuma akwai dalilai na addini ko aƙida. Amma a nan, kashi 99.9 na mu addinin mu ɗaya. To, me ake faɗaa kai?
Muna buƙatar dakatar da wasan nuna yatsa. A matsayina na gwamna, ba komai idan wani yana PDP, APC, ko baya goyon bayana. Kowa a Zamfara yana ƙarƙashin kulawa ta ne. Aikina shi ne na kare rayukansu da dukiyoyinsu. Don haka ina yin ƙoƙari na hankali, duk abin da ake buƙata, don dawo da zaman lafiya. Aiki ba sauƙi, amma za mu ci gaba da yi.
Shin za ka iya faɗaɗa shirye-shiryen ci gaban da ka ke ganin za su taimaka wajen samar da zaman lafiya?
Gaskiyar ita ce, yawancin waɗannan al'ummomin ba su da muhimman abubuwan - makarantu, ruwa da kiwon lafiya. Nawa zai ci a gina aji? Ko rijiyar burtsatse? Ɗan ƙanƙanin kuɗi ne. Sai na ce musu, zan samar da duka, a ba mu zaman lafiya.
Dole ne mu saka hannun jari a cikin ci gaba idan muna son tsaro mai ɗorewa. Gwamnatina ta mayar da hankali wajen samar da waɗannan ayyuka. Ta haka ne za mu canja labarin jihar.
Ayyukan tsaro na buƙatar kuɗaɗe, amma duk da haka Zamfara na samun ɗaya daga cikin mafi ƙarancin kaso daga Gwamnatin Tarayya. Yaya ka ke gudanar da al'amura?
Haka ne. Muna samun ɗayan mafi ƙarancin kaso. Amma tsaro shi ne ginshiƙin abin da muka sa a gaba, sai ilimi.
Dole ne mu san yadda za mu yi. Muna ɗaukar nauyin al'amuran tsaro ne ta hanya ɗaya zuwa wata. Muna kuma ɗauki nauyin CPG gaba ɗaya. A watan da ya gabata, mun sayi sabbin motoci guda 140 masu aiki — wasu masu kare harsashi, da sauran — muka raba su ga hukumomin tsaro. Ni da kaina na ba da tallafin man fetur da ayyukan su. Idan zan kashe kashi 80 na kuɗaɗen mu don samar da zaman lafiya, zan yi. Mutane sun cancanci su yi barci da idanun su biyu a rufe.
A lokaci guda, muna aiki don haɓaka kuɗaɗen shiga na cikin gida. Zamfara ta samu albarkar ma’adanai masu muhimmanci, musamman lithium, wanda za a iya cewa shi ne mafi inganci a duniya. Yanzu muna tsara fannin haƙar ma'adinai, tare da yin aiki tare da gwamnatin tarayya da abokan hulɗa masu zaman kansu. Wannan zai taimaka mana wajen samar da ababen more rayuwa, ilimi, da aikin yi.
Idan muka yi nasara, mutane za su zo daga Legas ko ma Brussels don neman zinariya da lithium na Zamfara.
Mun bi ta Funtuwa da Tsafe, wuraren da a da ake kira wuraren ’yan bindiga. Amma mun ga zaman lafiya. Shin shirin ka na Askarawan Zamfara ya ba da gudunmawa ga wannan?
Lallai. Tsafe, Funtuwa, Zurmi — waɗannan yankunan sun sami kwanciyar hankali a yanzu, saboda ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi. Wannan ya nuna cewa shirin yana aiki.
Kuma eh, na goyi bayan ra'ayin kafa 'yan sandan jiha. Na rubuta wa Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa cewa na bada cikakken goyon baya.
A matsayinmu na gwamnoni, ana kiran mu manyan jami’an tsaro, amma duk da haka ba mu da iko kan jami’an tsaro. Muna zaune a cikin waɗannan al'ummomin. Mun fahimci motsin su. Don haka, ya kamata mu iya ba da amsa ga barazanar tsaro da sauri.
Askarawan Zamfara rundunar tsaro ce ta cikin gida yadda ya kamata. Muna ɗaukar nauyin komai kama daga – motoci, albashi, rigunan lare harsashi, man fetur da dai sauran su. Muna kan gaba. Ayyukan na buƙatar tsari ne.
Kun ce kuna kan aikin ceto. Amma kai gwamnan Zamfara ne. Kana cewa Gwamna Matawalle da ya gabace ka bai yi komai ba?
To, ba zan ce bai tabuka komai ba. Amma a bayyane yake cewa abubuwa ba su yi tasiri ba. Shi ya sa na bayyana gwamnatina da cewa tana aikin ceto ne – don gyara abin da ya lalace, da sake gina cibiyoyi, da dawo da zaman lafiya, da kawo ci gaba ga jama’armu.
Zamfara ta faɗa ƙarƙashin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma da aka ƙirƙiro. Akwai kuma shirin ci gaban yanki na shekaru 10 da ya shafi sauran gwamnoni. Wane irin haɗin kai ka ke samu daga takwarorinka na Arewa maso Yamma?
Wannan tambaya ce mai muhimmanci. Rikicin Arewa maso Yamma ya shafe mu duka - Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa. Wani abin sha’awa shi ne, Kano da Jigawa sun yi nasarar kaucewa mafi yawan waɗannan matsalolin tsaro. Me ya sa? Tun daga farko, suna da haɗin kai a tsakanin mutanensu. Ba su kare masu laifi ba. Idan yaron wani ya yi laifi, sai su miƙa shi ga hukuma. Wannan tunanin ya taimaka musu wajen shawo kan yaɗuwar matsalar.
Don haka, a matsayinmu na gwamnoni, mun fahimci cewa akwai buƙatar a ƙara yin haɗin gwiwa. Kowannenmu ya ƙaddamar da Rundunar Tsaron Al'umma - Katsina ta fara, sai Zamfara, sai Sakkwato da Kebbi suka biyo baya. Amma bayan haka, muna kuma raba bayanai. Domin abin da ke faruwa shi ne, da zarar ka matsa wa ‘yan bindiga a wata jiha sai su koma wata jiha. Shi ya sa muke buƙatar dabarun haɗin gwiwa, ba rarrabuwar kawuna ba.
Kana gudanar da manufofin ƙin sulhu da 'yan bindiga. A halin yanzu dai jihohin da ke makwabtaka da kai – Katsina su kan yi sulhu. Shin hakan ba zai lalata haɗin kai ba?
Yana haifar da ƙalubale. Ina yawan cewa, duk wani shiri na zaman lafiya dole ne ya kasance cikakke. Idan za ka yi sulhu a Katsina a lokacin da nake takurawa a Zamfara, za su wuce can ne kai tsaye. Don haka muna buƙatar tsari guda ɗaya. Abin da nake ci gaba da gaya wa abokan aikina ke nan. Dole ne mu yarda da dabara guda kuma mu tsaya a kai.
Ka ba da shawara ga kafa 'yan sandan jiha. Amma masu suka suna kushewa da batutuwa kamar - kuɗaɗe da ba da umarni da dai sauran su. Mene ne amsar ka?
Na fahimci damuwar. Amma bari mu faɗi gaskiya - ko da tsarin 'yan sandan ƙasa ba rasa abubuwan kushewa. Maganar ita ce, 'yan sandan jihohi za su yi tasiri sosai saboda mutanen yankin sun fahimci al'ummominsu. Kuma game da kuɗaɗe, na yi imanin ya kamata jihohi su ɗauki nauyin tsaron su. Na riga na samar da tsari a bangaren kuma mutane sun shirya.
A bara, ka maddamar da aikin Dala Biliyan 11.7 ga yara mata masu tasowa. Shin ya yi tasiri?
Lallai. Mun gina manyan makarantu a faɗin ƙananan hukumomin uku a ƙarƙashin shirin AGILE. Yana taimakawa inganta ilimin yara sosai. Kuma maganar gaskiya ita ce, kafin zuwan mu Zamfara ba ta da fitilun rage cunkuson ababen hawa – babu abin hawa na 'lift' ko guda ɗaya. Amma yanzu, muna gina otel mai tauraro huɗu tare lift da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa. Waɗannan su ne ainihin abubuwan da ya kamata a yi tuntuni.
Ka ambaci kuɗaɗe. Ku na da PAYE, amma ku na samun kuɗaɗen shiga daga ma'adinai?
Wannan batu ne mai zafi. Ma'adinai babban abu ne, eh. Amma fili mallakin jiha ne. Don haka, na gaya wa Ministan Ma’adinai cewa dole ne mu samu tsarin aiki. Yanzu haka, Zamfara ba ta samun ko sisin kwabo daga haƙo ma’adinai. Ba naira ɗaya ba. Amma mu masu hankali ne. Ban ranci ko kwabo don ɗaukar nauyin ayyukanmu ba. Duk kwangilar da ka gani, an riga an ware kuɗin. Ba za a yi watsi da aikin ba.
A yau ne shugaba Tinubu ya ziyarci Benuwai. Me za ka yi idan kai ne a matsayin sa?
Tsaro ƙalubale ne gama gari a faɗin Arewa. Ko Zamfara, Binuwai, ko Filato, batutuwa iri ɗaya ne. Dole ne mu magance tushen matsalar. Dole ne mu haɗa kai a matsayinmu na shugabanni, mu ɗauki mataki mu kare al'ummarmu.
Mu ɗauke ka daga siyasa mu koma mulki. Kafin ka hau mulki, ma’aikatan gwamnati a Zamfara suna karbar Naira 7,000 a duk wata. Amma gwamnatin ka ce ta canja adadi. Za ka iya ƙarim haske a hakan?
Bari in gaya maka abin da ya fi doka na lokacin da na karbi ragamar mulki. Na farko, na samu bashin albashi na watanni huɗu – wanda aka ƙirƙira da gangan. Amma da na duba baitulmali, babu kuɗi. Kuma idan na gaya wa mutane cewa na Naira Miliyan 4 kacal na tarar, sai su yi dariya. Amma gaskiya ce. Ni ma'aikacin banki ne.
Lokacin da na hau mulki, albashin ma’aikaci a Zamfara Naira 7,000 na kacal. Na ce, ta yaya mutum zai tsira a kan haka? Don haka, bayan warware bashin albashin ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa, sai na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000.
Bayan haka, na gabatar da garabasar albashin ƙarin wata ɗaya, wanda ake kira albashi 'watan 13'. A watan Disamba, na biya ma’aikatan gwamnati alawus, kuma har yanzu ina yi. Yanzu N70,000 ne sabon mafi ƙarancin albashi, mun aiwatar da shi a matakin jiha da ƙananan hukumomi. Haka kuma muna ci gaba da biyan albashin watan 13 tare da bayar da ƙari a lokutan bukukuwa.
Nawa ka ci bashi tun lokacin da ka hau mulki, kuma ka na shirin ƙara karbar rance?
Bari in bayyana ƙarara, ni Dauda Lawal, Gwamnan Jihar Zamfara, tun da na hau mulki, ban ciyo ko kwbo daga wata cibiyar hada-hadar kuɗi ba. Yau 18 ga Yuni, 2025, kuma komai nawa na tafiya daidai.
Babu wata matsala dangane da karbar rance idan kana da ayyukan da za ka nuna idan ka karba. Amma ina adawa da rance da niyyar sata kawai. Yayin da muke magana, har yanzu ina biyan basussukan gwamnatin da ta shuɗe. Zan iya nuna maka takardun - Naira Biliyan 1.5 da ake cirewa kai tsaye, yanzu an rage zuwa Naira biliyan 1.118 daga rabon FAAC na ƙarshe.
KEDCO yana bin mu bashin Naira Biliyan 1.6 na wutar lantarki. Lokacin da na hau mulki, babu lantarki a ofisoshin gwamnati. Na biya bashin. Babu ko da mota ɗaya ga gwamna a lokacin da na hau mulki. An kwace ofishin hulɗarmu da ke Kaduna — sai da na biya Naira Miliyan 600 na karbo shi. Har yanzu muna gyara ofishin hulɗarmu na Abuja, amma ba wani fifiko ba ne domin na riga na samu gurbi a Abuja. Bugu da ƙari, ban aro ba, kuma ban shirya ba. Amma idan buƙatar ta taso a nan gaba, za mu yi la'akari da shi. A halin yanzu, muna da kwanciyar hankali.
Ka kuma yi magana a bainar jama'a game da buƙatar manufofin ƙasa don kare mutanen da ke gudun hijira (IDP). Mene hali ake ciki yanzu a Zamfara?
Mun yi jerin gwano da Ma’aikatar Agaji ta Tarayya. Kwanaki biyu kacal da suka wuce, jami’an ma’aikatar sun je Gusau domin tantance halin da ake ciki tare da duba yadda za su taimaka. Haka kuma mun fara gina cibiyoyi don sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ke da tazarar kilomita kaɗan daga wajen Gusau. Ƙoƙari ne mai gudana.
Ka saka jari da yawa a fannin lafiya. Shin kana tunanin rangwame daga wani asibiti? Mene ne shirin ka na samar da kiwon lafiya mai araha, musamman ga talakawa?
Mun tsara nau'o'i daban-daban - akwai tsarin inshora da tsarin ba da gudunmawa. Gwamnonin Jihohi da na Ƙananan Hukumomi suna sayen magunguna ga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da na biyu. Muna kuma gwada abin da ke aiki kuma muna sa ido sosai don hana rashin kulawa.
Ɗan kwangila ɗaya wanda ya gina asibitocin ya ba da shawarar tsari mai ɗorewa. Yana garin yanzu, kuma muna nazarin shawarwarinsa. Muna iya haɗawa da duk asibitoci, duka waɗanda aka kammala da masu gudana, ƙarƙashin tsarin gudanarwa mai ɗorewa.
Ka samu mulki bayan doguwar taƙaddamar shari'a, kuma Kotun Ƙoli ce ta yanke hukuncin marshe a kan ka. Yanzu haka dai Majalisar Dokokin Ƙasar na shirin mayar da Kotun Ɗaukaka Ƙara a matsayin kotun ƙarshe na yanke hakunci kan zaben gwamna. Mene ne ra'ayin ka?
Ba na so in yi zurfi cikin al'amuran majalisa, amma na yi imanin cewa dole ne mu yi taka tsantsan kafin mu hanzarta yanke hukunci. Mutane irin mu, masu ƙwarewa, yakamata a tuntube su.
Mene ne saƙonka na ƙarshe ga al’ummar Zamfara na gida da waje?
Ina miƙa godiyata ga al'ummar Zamfara bisa goyon bayan da suka ba mu da fahimtar juna tun daga rana ta farko. Ina roƙon su da su ci gaba da ba mu goyon baya domin mu ci gaba da samar da ribar dimokuraɗiyya. Ga waɗanda ke cikin ƙasashen waje, muna aiki don ƙirƙirar yanayi wanda zai ja hankalin ku don dawowa. A bangaren kiwon lafiya, alal misali, mun fara ba da kayan tallafi na kyauta don ƙarfafa gwiwar ƙwararrun likitoci da su dawo su yi aiki a Zamfara.
Me jama'a za su yi tsammani a cikin sauran shekaru biyu na ka?
Ƙarin abubuwa masu kyau. Ina da yaƙinin idan kun dawo lokaci na gaba, za ku ga jihar Zamfara gaba ɗaya ta canja. Wannan shi ne burina, kuma zan ci gaba da mai da hankali kan aiwatar da shi.
No comments