Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kano Ya Nuna Kyakkyawan Misali Wajen Kyauta Wa Alhazai -Alhaji Muhammad Mashakur

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa jagora ne da ya nuna kyakkyawan misali wajen yin...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa jagora ne da ya nuna kyakkyawan misali wajen yin hidima ga Alhazai  a matsayin sa na Amirul Hajji na jihar Kano a aikin Hajjin bana.

Alhaji Muhammad Hussain Mashkur Gwangwazo, ɗan kasuwa a jihar Kano, kuma hadimin Gwamnan Kano Abbas Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai, ya ƙara da cewa tafiyar sa aikin Hajji ya bai wa shugabanni misali a matsayin sa na lamba ɗaya, ya cire rigar mulki ya shiga cikin ma'aikata yana yi wa Alhazai hidima.

Ya ce, yadda Gwamnan Kano ya shiga ana aiki da shi domin ya tabbatar ana yin abu na inganci da kyautata jin daÉ—in Alhazai yadda ya kamata, kuma komai ya tafi daidai. Don haka Gwamnan ya cancanci a jinjina masa kan wannan kyakkyawan aiki da yi masa addu'a Allah ya taimake shi ya ci gaba da ba shi nasara.

Alhaji Muhammad ya yi nuni da cewa daga abin da ya ba shi sha'awa shi ne yadda Gwamna da ya ke da hidima kansa ya riƙa yi wa Alhazan jihar Kano aikace-aikace, ya shiga cikin masu aikin abinci ake yi da shi, babu jin cewa shi Gwamna ne, ƙoƙarinsa yaya za a kyautata wa waɗanda suka je aikin Hajji.

Ya ce, sannan kuma ya bada tallafin kuÉ—i na Riyal 100 ga kowane Alhaji na jihar Kano wanda  kowanne sai da ya sami abin da in aka kwatanta da Naira an ba shi ₦125,000 wannan ba Æ™aramin abin alkhari ba ne da Alhazai suka ji  daÉ—in sa.

Ya ce, ya kamata masu mulki ko muƙarraban Gwamnati da aka zaba su jagoranci Alhazai a ƙasar nan su yi koyi da irin wannan kyakkyawan misali da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna a aikace.

Alhaji Muhammad Hussain ya ce cikar Gwamna Abba Kabir Yusuf shekara biyu akan mulki tun daga rantsar da shi sun gamsu sosai da yadda yake tafiyar da ayyuka, domin ya zo ya yi abin da Gwamnatin baya da ta shekara Takwas ba ta yi ba, ya cancanci yabo da jinjina.

Daga nan Alhaji Muhammad Hussain Mashkur ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da cewa sun ga misali na irin ɗimbin ayyuka da Gwamna yake gudanarwa a ko'ina a sassan jihar Kano, kuma an ce daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Don haka ba sai an ce ga abin da za su yi ba, illa shawara da zai ba su, su karkaɗe ƙuri'un su su ajiye shi har Allah ya kai mu zaben 2027 a sake kaɗa ƙuri'a ga Injiniya Abba Kabir Yusuf a karo na biyu.
 

No comments