Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za A Inganta Ƙungiyar Wasannin Ƙwallon Ƙafa Ta Kaduna United -Sa'idu Bidis

Daga Imrana Abdullahi Malam Sa'idu Idris Dibis, mataimaki ne na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin wasanni, ya bayyana cewa...

Daga Imrana Abdullahi

Malam Sa'idu Idris Dibis, mataimaki ne na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin wasanni, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar, ƙarƙashin jagorancin Malam Sanata Uba Sani za ta samar da sahihiyar ingantacciyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta "Kaduna United" domin ƙara inganta tattalin arzikin Jihar.

Sa'idu Idris Dibis da ake yi wa laƙabi da Koch, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala gasar ƙarshe ta wasan ƙwallon pafa da JKD Academy suka shirya a tsakanin makarantun Sakandaren da ke cikin garin Kaduna.

Dibis ya ce haƙiƙa wannan rana da aka buga wasan ƙarshe na wannan Kofi, ya zo daidai da ranar da ake ta bikin murnar samun nasarar Gwamna Uba Sani a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kaduna, kamar yadda Kotun ƙolin  Nijeriya ta tabbatar masa. 

Ya ce kuma, gasar ta zo daidai da ranar da Mahaifin waɗannan yara da suka sanya wannan kofi, ya zo daidai da ranar haihuwar sa, wato Dattijo Ambasada Yusuf Mamman, da yake cika shekaru Saba'i. "Don haka muna yi wa Allah godiya a kan hakan, bisa gamsuwa da farin cikin da nake ciki ƙwarai.

"Akwai aikace-aikacen da Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya a gaba da nufin farfaɗo da harkokin wasanni a Jihar Kaduna.

"A cikin watanni Bakwai ko Takwas, an fara samun tagomashi a harkokin wasanni a Jihar Kaduna. Akwai shirye shirye-shiryen da ake yi domin bunƙasa harkokin wasanni a Jihar Kaduna.

"Za a yi gudu, wato tseren Dawaki, wanda tuni har Gwamnan Jihar Kaduna ya bayar da damar a ƙaddamar da shi domin murnar cika shekaru uku na Mai martaba Sarkin Zazzau, wanda lamarin zai zamo kamar na farko ne a Jihar Kaduna. 

"Kuma da ikon Allah a ƙarshen watan biyu za a ƙaddamar da wasan, har tsawon kwanaki uku, muna fatan 'yan jarida za su taimaka mana wajen samun nasarar hakan".


Dibis ya kuma ƙara jaddada cewa, "Haka zalika, muna yin kyakkyawan shiri a kan samun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kaduna United, kuma ba ta Gwamnati zalla ba, ta 'yan Kasuwa da Gwamnati, wanda ba za ta zamo a buga ba ne, kawai muna son ta zamo kamar kasuwanci.

 

No comments