A cikin wata sanarwa da ƙungiyar Dattawan Arewa ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ƙungiyar, Abdul-Azeez Suleman, ta bayy...
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar Dattawan Arewa ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ƙungiyar, Abdul-Azeez Suleman, ta bayyana cewar mayar da wasu ɓangarori na babban bankin ƙasar nan na CBN zuwa Legas zai raunata ƙarfin tattalin arziki na birnin tarayya Abuja, don sam ba ta amince da hakan ba.
Kungiyar ta ƙara da cewar, mayar da wasu sassan bankin zuwa Legas zai shafi ci gaban tattalin arziki na Nijeriya gaba ɗay, kuma zai ƙara haifar da tashin gwauron zabi na kayayyaki, sannan uwa-uba zai mayar da yankin Arewa baya.
Ƙungiyar ta ja hankalin Bankin akan wannan matakin da ake shirin ɗauka da cewar zai tursasa wa wasu Ma’aikatan bankin yin ritayar dole.
Sanarwar ta ƙara da cewar, “Ƙungiyar Dattawan Arewa ta damu matuƙa da rahoton yunƙurin mayar da wasu manyan ɓangarorin bankin daga Abuja zuwa tsohuwar shalkwatar bankin da ke birnin Legas”.
Ƙungiyar ta bayyana cewar manyan sassan da ake yunƙurin mayar wa Ikko, wannan abin tambaya ne, waɗanda suka haɗa da ɓangaren sa-ido kan bankuna DBS, da cibiyoyin sa-ido kan cinikayya OFISD, da ɓangaren kariya ga abokan hulɗa CPD, da sauran manyan ɓangarori.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewar mayar da waɗannan manya, kuma muhimman ɓangarori zuwa Legas zai zama an ƙara ƙarfafa Legas da yankin Kudu ne, yayin da a hannu guda kuma an naƙasa Abuja da yankin Arewa.
Don haka suka yi kira ga Shugaban Tinubu da ya canja wannan tunani nasa, ya nwmi haɗin kan ƙasa.
No comments