Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Marayu Da Ɗaliban Tsangaya 110 Suka Amfana Da Tallafin 'Kafilatul Mahabbah' A Funtuwa

Daga Hussaini Yero, Funtua Cibiyar 'Kafilatul Mahabba' ta ƙasa reshen Ƙaramar Hukumar Funtuwa, ƙarƙashin jagorancin shugaban Cibiyar...

Daga Hussaini Yero, Funtua

Cibiyar 'Kafilatul Mahabba' ta ƙasa reshen Ƙaramar Hukumar Funtuwa, ƙarƙashin jagorancin shugaban Cibiyar na ƙasa, Farfesa Ibrahim Makari ta ba Marayu Maza da Mata da ɗaliban Makarantun tsangaya tallafin kayan sanyawa su ɗari da goma.

Shugaban Cibiyar na reshen Funtuwa, Barista Ahmad Tijjani Magaji ya bayyana cewa, ayyukan wannan ƙungiya, sun haɗa da shirya taruruka a wasu muhimman ranaku da ake da su a cikin shekara. "Don haka yau ce ranar Yaumul Kiswa, shi ne  muka ga ya dacemu rayata da tallafin kayan sawa ga marayu da ɗaliban Tsangaya, don su ma su amfana,"ya ce.

Ahmad Tijjani ya kuma ƙara bayyana ayyukan Cibiyar kamar, Ziyartar Asibitoci, ba Masara lafiya tallafi tallafi, ziyara gidan gyaran hali da gangamin tsaftace muhalli a ƙarshen kowane wata.

Malam Yusuf Lawandi, shi ne shugaban Cibiyar Riyadu Salihu, tare da Malam Gazali ne suka gabatar da ƙasidu akan muhimmancin bada tallafi a addinin Musulunci, kuma sun gargaɗi mawadata akan riƙe abin hannun su ga mabuƙata, wanda wannan yana tauye arziki mawadaci.

Kuma sun Jinjina ma Kafilatul Mahabba wajen taimakon al'umma, lallai abin koyi ne da wannan Cibiya a Funtua da ƙasa baki ɗaya.

Shugaban Kwamitin zagayen gari na Maulidin Annabi (s) na Funtuwa, Muhammad Busiri da ya samu wakilcin ma'ajin ƙungiyar, Alhaji Bashir Yero, ya bayyana cewa, wannan Cibiyar ta zo daidai lokacin da ya dace, don yanzu lokacin ne da al'umma ke cikin matsi na rayuwa da suke buƙatar tallaf. 

"Muna jinjina da godiya ga iyayan wannan Cibiya ta ƙasa da suka kawo abin arziki a cikin mu, Allah ya albarkaci wannan Cibiya ya sanya ƙudirinta ya cika na tallafa wa al'umma amin.

A nasa jawabin, Sakataren Cibiyar na Ƙaramar Hukumar Funtuwa, Zaharaddini Ibrahim ya bayyana cewa, wannan ƙungiya tana samun kuɗin shiga ne daga mambobin ta, ba su zuwa ko'ina don neman taimako, amma duk wanda ya kawo taimako za su amsa hannu biyu.

 

No comments