Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Boko Haram Ta Farmaki Sansanin Sojoji, Ta Kashe Hafsan Soji A Borno

Mayaƙan Boko Haram sun kashe wani hafsan soja da wasu ’yan sa-kai biyu a wani ƙazamin hari a sansanin sojoji a Jihar Borno. Wata majiyar soj...



Mayaƙan Boko Haram sun kashe wani hafsan soja da wasu ’yan sa-kai biyu a wani ƙazamin hari a sansanin sojoji a Jihar Borno.

Wata majiyar soji ta shaida mana cewa an kasa ɗauko gawar waɗanda aka kashe, saboda tsananin faɗan da aka gwabza da misalin ƙarfe 1 na dare a sansanin da ke yankin Krenowa a Ƙaramar Hukumar Marte ranar Asabar.

Ta ƙara da cewa, maharan sun lalata wata motar yaƙi, amma direbanta ya tsira da rauni a ƙafarsa, sannan sojoji fiye da 100 tare da makamai da sauran kayan aikinsu sun janye zuwa garin Marte.

Wasu majiyoyi sun shaida w manema labarai cewa mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojojin hari ne kwanaki biyar bayan sojojin sun ƙwace sansanin ƙungiyar da ke Krenowa a ƙoƙarin sojojin na kakkaɓe ’yan ta’adda.

No comments